Labaran YauNEWS

Antashi Baram-Baram Tattaunawan Gomnatin Tarayya Da Malaman Jami’a

Antashi Baram-Baram Tattaunawan Gomnatin Tarayya Da Malaman Jami’a

An gaza cimma matsaya a zaman tattaunawa tsakanin wakilan gwamnatin tarayya da na kungiyar Malaman Jami’o’i ‘ASUU’ wanda hakan ke nufin malaman zasu ci gaba da yajin aikinsu wand aya shafe tsawon watanni biyu ana yi kenan.

Kungiyar Malaman reshen Abuja ta hannun wakilinta Dakta Salahu Muhammad, ta bayyana cewa a shirye Malaman suke so dawo bakin aikinsu, muddin aka cika musu alkawuran da aka dauka tun a shekarar 2009.

DOWNLOAD MP3

Dakta Salahu ya bukaci iyaye da dalibai su gaggauta jawo hankalin Ministan Sadarwa, da Shugaban Hukumar NITDA da su amince da tsarin biya da Malaman suka fi amincewa da shi, wato tsarin UTAS, wanda kungiyar ke zargin Ministan Sadarwa da Shugaban NITDA da neman yin fatalk da shi ba tare da wani gamsasshen dalili ba.

Malaman suna ganin da gangan shugaban NITDA ya ki amincewa da tsarin na UTAS, wanda a cewarsu tsarin yana da inganci fiye da wanda gwamnatin tarayya take amfani da shi na IPPIS, wanda yana daga cikin abubuwan da Kungiyar take kalubalantar gwamnatin tarayya a kan shi.

DOWNLOAD ZIP

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button