Labaran TuranciNEWS

Ankai Harin Bomb Wata Mashaya A Jihar Taraba

Ankai Harin Bomb Wata Mashaya A Jihar Taraba

Bam ya kashe mutum biyar a Jihar Taraba

Wani harin bam da aka kai a wata mashaya da ke Jihar Taraba a gabashin Najeriya ya kashe aƙalla mutum biyar.

Wasu 19 sun samu munanan raunuka sakamakon fashewar wani abu a garin Iware.

Shaidu sun ce an ɓoye bam ɗin ne a cikin wata jaka.

Lamarin ya faru ne da tsakar ranar Talata yayin da mutane suka taru a majalisar da ake shan barasa.

Rundunar ‘yan sandan jihar sun shaida wa manema Labarai cewa ɗaya daga cikin wadanda ake zargi da kai harin ya mutu, amma ba a sani ba ko ɗan ƙunar-bakin-wake ne.

Tashin bomb din yazo da Matukar abin alajabi dubi da jimawan da akayi a kasar Nijeriya  bomb bai tashi ba.

Saidai haryanzu ba’a gano wanda alhakin kai harin ke kansu ba, kuma bawata Kungiya data dauki nauyin kai harin.


Discover more from Labaran Yau

Subscribe to get the latest posts sent to your email.

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Discover more from Labaran Yau

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading