
Jaririn da aka yi watsi da shi a karkashin bishiya a Bauchi.
An tsinci jariri sabon haihuwa a yashe a karkashin wata bishiya kusa da wani asibiti a karamar hukumar Shira a jihar Bauchi.
A cewar wani malamin firamare Auwal Maisalati Shira, an bar jaririn akan ganye a karkashin bishiyar da ke kusa da Asibitin Ambara da misalin karfe 12 na rana a ranar Laraba 16 ga watan Agusta, 2023.
An tsinci jaririn a cikin wata atamfa ta zanin mata, sanye da kayan sa masu kyau a jikin sa.
Malam Auwal ya ce shi da jami’in jin dadin jama’a na karamar hukumar Shira ne suka kai jaririn zuwa dakin haihuwa na asibitin.