
Yadda Ake Yar Tsame
Yar tsame abinci ne wanda aka fi yi a arewacin kasar Najeriya.
Garuruwa irinsu Gombe, Bauchi da sauransu neh sukafi yin yar tsame a matsayin abinci. Ga Yadda ake sarrafa Yar tsame cikin kankanin lokaci.
Kayan Hada Yar Tsame
1. Gero nikakke gwangwani 4
2. Yeast 1 karamin cokali
3. Baking powder
4. Gishiri
5. Karkashi babban cokali 1
6. Albasa 1
7. Flour gwangwani 1
Yadda Ake Hada Yar Tsame
- A surfa geron sai a wanke yafita sosai
- Ayanka albasa a akai nika
- In andawo kizuba yeast, baking powder, gishiri kadan, flour sai a motsa karyayi ruwa ruwa kuma karyai kauri sosai kamar kaurin koko,
- Se abarshi yatashi kamar 30mins ko 1hr
- A zuba mai cikin frying pan a daura a wuta in yayi zafi
- Afara zubawa da ludayi ko cokali babba in gefe daya yai ajuya dayan gefen din shima inyayi se akwashe.
Ana cii da yaji ko kuli kuli