
Abinda yasa yawancin mutane suke gagara yin miyan ridi koda sunyi bata yin dadi shine basu bin tsarin girkin yanda yadace wasu kuma basu saka sinadaren yanda yakamata.
Biyoni domin samun cikakken bayanin yanda ake girka miyan ridi.
Kayan Hada Miyan Ridi
1. Manja
2. Maggi
3. Gishiri
4. Kaza
5. Nikekken ridi
6. Tattasai
7. Attaruhu
8. Albasa
10. Ganyen ogu
11. Citta
12. Tafarnuwa
13. Daddawan inyamurai
Yadda Ake Girka Miyan Ridi
- Za a sa nikkaken ridi a kwano a yayyafa mai ruwa
- Sai a yita murzashi har sai ya fidda mai kamar yadda ake fidda man agushi sai a ajiye a gefe
- A dauki kaza ko nama a wanke a sa tukunya asaka tafarnuwa, albasa, Maggie, citta gishiri a dafa shi dasu sai a ajiye shi a gefe
- Sai a daura tukunya a sa maja a ciki a yi blichin din shi wato har sai yayi fari sai a sauke shi kasa ya huce
- Sai a markada kayan miyan tattasai, attaruhu da albasa kar yayi laushi
- A zuba a cikin manjan da ya huce a mayar kan wuta.
- A zuba daddawan inyamurai asoya su tare, idan ya soyu sai a zuba ruwan naman tare da naman, maggie da gishiri idan ya tafaso
- Sai a faffasa dunkulallen ridin da aka cire mai a ciki sai a wanke ganyen ogu a yanka a zuba Shima ba a sa ganyen dayawa kadan ake sawa saboda ana so yayi daddaya daddayane sai a juya a rufeshi
- Sai a bashi minti ashirin ya dafu sannan sai a sauke.
Ana cin shine da tuwon shinkafa,semovita ko sakwara.