Labaran Turanci

“Dalilin Da Ya Sa Na Daina Yin Shigar Mata A Cikin Skits Na” – Josh2funny Ya Bayyana

Shahararren dan wasan barkwanci kuma skitmaker Josh2funny ya bayyana ainihin dalilin da ya sa ya daina sanya sutura mata a cikin sket bidiyon sa.

Josh2funny dai dan Najeriya neh daga jahar Anambra, Josh ya kasance mutum meh bawa mutane dariya shahararre ne wajen barkwanci ta sifar mata.

A cikin wata hira da aka yi kwanan nan akan podcast din Honest Bunch, ya bayyana cewa ya sami ci gaba maras dadi daga magoya bayanshi yayin da yake nuna kansa a matsayin Mama Felicia cikin bidiyoyinsa.

Ya ce ya yanke shawarar yin watsi da salon Mama Felicia don ya ɗauki sifar maza amatsayin Zacchaeus don ya daina jin kunyar da yake ji.

Ga abinda ya fada a Podcast din Honest Bunch daga bisani ⇓

“Ka ga, ban-banci da ke tsakanina da wasu mutanen da ke da halin mace, nawa wasan kwaikwayo ne kai tsaye.

Duk wanda ya ganni kallon wanda ba ya da hankali sosai yakemin, ban san inda abin zai dosa ba saboda na tabbatar wauta ce,” in ji shi.

“Mama Felicia wauta ce, wauta ce na gaske. Na sami ci gaba da yawa.

Akwai guy haka, ban sanshi ba mutumin ya shigo whatsapp dina ya kalli kamar ni yacemin ina sonka, kai tsaye na nufo shi nace bro zan yi Addu’a sai ka makance nan da sati biyu, mutumin ya fara rokona.

Toh ta yaya zai ganni, kamar ni? Yace yana sona?

“Shine na chanja salon comedi na daga Mama Felicia ce na juya Ɗan’uwa Zacchaeus. Maimakon in sa rigar mata, sai na sauke na fara sanya tufafin maza, ina amfani da lafazi iri ɗaya.

Ya zama abin kunya a gare ni domin ina nufin in sa mutane dariya ne kawai.”

Asalin sunansa shine Josh Alfred, Josh2Funny ya ya samu daukaka ne lokacin da ya sake skit din #DontLeaveMe wanda ta zagaya yanar gizo da sauri kota ena.

A cikin watan Agusta 2023, ya ɗauki wasan barkwancinsa zuwa matakin duniya ta hanyar yin ɗaya daga cikin ƙwararrun haruffansa, “mafi sauri karatu a duniya”, akan Got Talent na Amurka.

Ga bidiyon Josh2fuuny a matsayin Mama Felicia daga bisani ⇓

 

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Watch African Stories

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button