Girke GirkeLabaran Yau

Yadda Ake Hada Miyan Ridi

Yadda Ake Miyan Ridi Cikin Karamin Lokaci

Kayan Hadi 

Manja

Maggi

Gishiri

Kaza

Nikekken ridi

Tattasai

Attaruhu

Albasa

Ganyen ogu

Citta

Tafarnuwa

Daddawan inyamurai

Yadda Ake Hadawa

Za a sa nikkaken ridi a kwano a yayyafa mai ruwa sai a yita murzashi har sai ya fidda Mai kamar yadda ake fidda man agushi sai a ajiye a gefe , sai a dauki kaza a wanke a sa a tukunya a sa tafarnuwa,albasa, Maggie, citta gishiri a dafa shi dasu   sai a ajiye shi a gefe

Sai a daura tukunya a sa maja a ciki a yi blichin din shi wato har sai yayi fari sai a sauke shi kasa ya huce , sai a markada kayan miyan tattasai, attaruhu da albasa kar yayai laushi sai a zuba a cikin manjan da ya huce a mayar kan wuta, sai a zuba daddawan inyamurai asoya su tare, idan ya soyu sai a zuba ruwan naman tare da naman,Maggie da gishiri idan ya tafaso sai a faffasa dunkulallen ridin da aka cire Mai a ciki sai a wanke ganyen ogu a yaka a zuba Shima ba a sa ganyan dayawa kadan ake sawa saboda ana so yayyi daddaya daddayane  sai a juya a rufeshi

Sai a bashi minti ashirin ya dafu sannan sai a sauke.

Tuwo Da Miyan Ridi
Tuwo Da Miyan Ridi

Ana cin shine da tuwon shinkafa,semovita ko sakwara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button