
Yadda Ake kosan Rogo
Ita kosan rogo abinci ne wanda aka fi yin shi a kasar hausa, ita kosar Rogo Ana yin ta da garin kwaki ne.
Ga takaicaccan bayani game da kosan rogo saboda bata da wuyan yi.
Kayan Hadi
1. Garin rogo(garin kwaki) Kofi biyu
2. Attaruhu kamar
3. Maggie
4. Onga(stew) guda daya
5. Mangyada Gwangwani daya
6. Albasa
Yadda Ake Hada Kosan Rogo
- Dafarko zaa tsince baki baki a garin da kuma kasa kasa dake ciki in akwai,
- Sai a juye a turmi asa ruwan zafi kadan a daka haka idan da rogon ne zaayi a yayyanka kanana asa a turmi a daka, har Sai ya kama kanshi yayi laushi.
- A jajjaga attaruhu yan kanana a zuba kamar guda biyar in manya ne a zuba guda uku depending on irin zafin attaruhun
- Albasa shi kuma in manya ne a saka babba guda daya in kanana ne a saka guda uku ,
- Maggie guda uku ko hudu yadda zai yi, onga stew guda daya ,a zuba Akai a daka sosai yayi Danko.
- Sai a kwashe ana dan marawa, kamin nan an saka tukunyar suyar a wuta an zuba mangyadar ta danyi zafi
- Sai a fara sakawa ana soyawa amai idan ya soyu a kwashe
Ana ci ta garin kuli kuli ko yaji