KannywoodEntertainment

Jaruman Kannywood da Suka Koma Nollywood

Jaruman Kannywood da Suka Koma Nollywood Saboda Wasu Dalilai Ne Kamar Samun Dama Mai Kyau, Kudin Shiga Mai Yawa, Da Kuma Cigaban Aikinsu.

A cikin ‘yan shekarun nan, an ga yadda wasu manyan jaruman Kannywood suke komawa Nollywood don cigaba da aikinsu a harkar fim.

Akwai dalilai da dama da suka sa hakan ke faruwa, kamar girman kasuwar Nollywood, samun damar fitowa a fina-finan duniya, da kuma matsalolin da ke cikin Kannywood.

Jaruman Kannywood da Suka Koma Nollywood

1. Ali Nuhu

2. Rahama Sadau

3. Uzee Usman

4. Sani Danja

5. Yakubu Mohammed

6. Maryam Booth

7. Amal Umar

8. Lilian Bach

Kuna Bukatar: Jerin Sabbin Finafinan Kannywood Masu Kayatarwa Na Soyayya, Ban Dariya, Ban Tausayi Dana Tarihi 2025

1. Ali Nuhu

Jaruman Kannywood da Suka Koma Nollywood
Ali Nuhu Yana Daya Daga Cikin Jaruman Kannywood da Suka Koma Nollywood

Ali Nuhu, wanda ake kira da Sarki na Kannywood, ya kasance daga cikin ‘yan wasan farko da suka fara shiga fina-finan Nollywood.

Ya fito a fim din “Banana Island Ghost”, “Last Flight to Abuja” tare da Omotola Jalade-Ekeinde da Jim Iyke. Har ila yau, yana fitowa a fina-finai da aka hada jaruman Kannywood da Nollywood.

Koda Kana Bukatar: Fitattun Jaruman Kannywood Masu Tashe a 2025

2. Rahama Sadau

Jaruman Kannywood da Suka Koma Nollywood
Rahama Sadau Tana Daya Daga Cikin Jaruman Kannywood da Suka Koma Nollywood

Rahama Sadau ta fara fitowa a Nollywood bayan da aka dakatar da ita daga Kannywood a shekarar 2016.

Ta taka rawar gani a shirin “Sons of the Caliphate”, “Hakkunde”, da kuma fim ɗin “The Milkmaid”, wanda ya samu shahara a duniya.

Rahama Sadau ta yi aiki da manyan jaruman Nollywood kamar Ramsey Nouah da Sola Sobowale.

Kuna Bukatar: Manyan Kamfanonin Kannywood dake Daukar Sabbin Jarumai | Hanyoyin Shiga Masana’antar Fim

3. Uzee Usman

Jaruman Kannywood da Suka Koma Nollywood
Jaruman Kannywood da Suka Koma Nollywood

Uzee Usman ɗan wasan kwaikwayo ne kuma mai shirya fina-finai wanda ya yi fice wajen haɗa masana’antar Kannywood da Nollywood.

An san shi da fina-finai kamar “Oga Abuja”, wanda ya samu lambar yabo ta Best Hausa Movie of the Year a City People Entertainment Awards na 2013.

Hakanan, fim ɗinsa “Maja” ya ci Best Film of the Year (Kannywood) a 2014. A shekarar 2021, an ba shi digirin girmamawa daga Iheris University, Togo, saboda gudummawarsa ga harkar fina-finai.

4. Sani Danja

Jaruman Kannywood da Suka Koma Nollywood
Sani Musa Danja Yana Daya Daga Cikin Jaruman Kannywood da Suka Koma Nollywood

Sani Musa Danja fitaccen jarumi ne wanda ya fara acting a Kannywood tun a shekarar 1999. Daga bisani, ya shiga Nollywood inda ya fito a fina-finai kamar “Daughter of the River” a 2012.

Hakanan, ya taka rawa a fina-finai kamar “Wives on Strike: The Revolution” (2017) da “Omo Ghetto: The Saga” (2020).

Koda Kana Bukatar: Jerin Jarumai 14 Mafiya Arziki A Kannywood 2025

5. Yakubu Mohammed

Jaruman Kannywood da Suka Koma Nollywood
Yakubu Mohammed Yana Daya Daga Cikin Jaruman Kannywood da Suka Koma Nollywood

Yakubu Mohammed ya shahara a Kannywood kafin ya samu damar fitowa a shirye-shiryen Nollywood kamar “Shuga Naija”, “Sons of the Caliphate”, da “4th Republic”.

6. Maryam Booth

Jaruman Kannywood da Suka Koma Nollywood
Maryam Booth Tana Daya Daga Cikin Jaruman Kannywood da Suka Koma Nollywood

Maryam Booth ta taka muhimmiyar rawa a fim ɗin “The Milkmaid”, wanda fim ne na Nollywood da aka yi da nufin nuna matsalar ta’addanci a arewacin Najeriya.

Kuna Bukatar: Jerin Sabbin Fina-Finan Kannywood 2025: Fitattun Fina-Finai Masu Tashe

7. Amal Umar

Jaruman Kannywood da Suka Koma Nollywood
Amal Umar Tana Daya Daga Cikin Jaruman Kannywood da Suka Koma Nollywood

Amal Umar ta samu damar fitowa a fina-finai daga bangaren Kannywood zuwa wasu shirye-shiryen da ke da hadin gwiwa da jaruman Nollywood.

8. Lilian Bach

Jaruman Kannywood da Suka Koma Nollywood
Lilian Bach Tana Daya Daga Cikin Jaruman Kannywood da Suka Koma Nollywood

Lilian Bach an fi sanin ta a fina-finan Nollywood, Lilian Bach ta yi fina-finai da yawa a Kannywood a baya, wanda hakan ya sa ake kallonta a masana’antun biyu.

Koda Kana Bukatar: Sabbin Fina-Finan Kannywood Masu Tashe a Shekarar 2025

Fina-Finai da Suka Haɗa Jaruman Kannywood da Nollywood

1. “Last Flight to Abuja”:

Wannan fim ɗin ya haɗa jaruman Nollywood kamar Omotola Jalade-Ekeinde da kuma jaruman Kannywood kamar Ali Nuhu.

2. “Sons of the Caliphate”:

Wannan shirine mai dogon zango inda ya hada jaruman Kannywood kamar Rahama Sadau tare da jaruman Nollywood, fim di ya kunshi labarin siyasa da al’adun arewacin Najeriya ne.

3. “The Milkmaid”:

Fim ne da ya samu lambobin yabo da dama, wanda ya haɗa jaruman Kannywood kamar Maryam Booth da kuma jaruman Nollywood, yana nuna labarin mata biyu da suka tsinci kansu a hannun ‘yan ta’adda.

Dalilan da Yasa Wasu Jaruman Kannywood ke Komawa Nollywood

1. Damuwa da takunkumin hukumar tace fina-finai

2. Neman damar shiga kasuwar fim ta kasa da kasa

3. Neman karin kudaden shiga da sabbin damarmaki

4. Rikice-rikicen cikin masana’antar Kannywood

Kuna Bukatar: Manyan Jaruman Kannywood Masu Tashe: Sunayensu, Tarihinsu da Abubuwan da Ke Jan Hankalin Masoya

Kammalawa

Yawancin jaruman Kannywood suna komawa Nollywood ne saboda samun dama mai kyau, kudin shiga mai yawa, da kuma cigaban aikinsu.

Amma har yanzu, suna da alaka da Kannywood kuma wasu suna dawowa don yin fina-finai a masana’antu biyu.

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Watch African Stories

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button