
Duk wanda yake kishin jahar Bauchi kuma yakeso yaga cewa an samu cigaba da bunkasuwar tattalin arziki dole ya yabawa Gomna akan aikin fly over daya saka agaba.
Fly over musamman awajajen cinkosu yanada matukar amfani saboda hanyane wanda yake kawo saukin yin abubuwa.
Ga wandanda basu saniba ga muhimman amfanin fly over guda biyar ga Jahar Bauchi
1. Rage cunkoson ababen hawa
Yankunan kasuwani suna fuskantar cunkoson ababen hawa saboda hada hadan kasuwanci, wanda ke haifar da matsaloli da dama. Gadar sama zai taimaka wajen sauƙaƙa cunkoso ta hanyar samar da hanyoyi wa manyan motoci da saukin zirga zirga.
2. Haɓaka Tsaro
Gadar sama ya raba hanya ma ababan hawa da masu tafiya a ƙafa, kuma tana rage hadurra a tituna da kuma tabbatar da tafiya cikin aminci.
3. Haɓaka Tattalin Arziƙi
Samun shimfidaddiyar hanyar sama zai saukaka wa yan kasuwa wajen karban kayayyaki daga abokan cinakansu. Kuma zaisa mutane suna sayan kayyaki ba tareda wani hayaniya ba.
4. Inganta Taimakon Gaggawa
Kasuwanni wuraren cunkoso neh wanda iftila’i zai iya barkewa a koda yaushe. Gadar sama zai bada damar kai gudumawa kamar na motocin daukar marasa lafiya da motocin kashe gobara.
5. Haɓaka Abubuwan Rayuwa
Gadar sama na jawo zata janyo ƙarin saka hannun jari a jahar yanda yan kasuwa zasuga saukin shigo da kayansu wa yan kasuwa. Allah ya taimaki jahar Bauchi.
Ga hotunan yanda aiki keh gudana daga bisani