KannywoodLabaran Yau

Matata Ummi Rahab Ta Tsallake Rijiya Da Baya – Lilin Baba

Matata Ummi Rahab, Ta Tsallake Rijiya Da Baya, Mun Gode Wa Allah, Cewar Mawaƙi, Lilin Baba

Shahararren Mawaki da akafi sani da suba Lilin Baba ya yi wata posting mai zafi da ya janyo cece kuce gami da muhawara a kafafen sadarwa na zamani.

Lilin Baba ya saki hotonsa ne tare da matarsa Ummi Rehab a shafinsa na Instagram inda ya yi wani rubutu cikin harshen Turanci da ke cewa

My wife-Ummi Rehab, has really dodged a bullet. Thank God!”, ma’ana “Alhamdulillah! Matata Ummi Rehab ta tsallake rijiya da baya”

 

Duk da dai bamusan meya faru da Ummi ba amma ana ganin cewa Lilin Baba ya yi habaici ne ga Adam A Zango a wancan rubutun mai dauke da hoton nasa da Rahab, bayan da jarumi A Zango ya sanarwa da duniya halin da a ke ciki tsakaninsa sa da matarsa Safiyya.

Lokacin da Zango yake bayani akan aurensu, Idan ba a manta ba Adam Zango dai shi ne wanda ya raini Ummi Rahab a masana’antar Kannywood, wanda daga karshe suka samu sabani har aka raba gari tsakaninsu.

Daga irin zargin da Ummi ta yiwa Zango kafin rabuwar ta su, shi ne cewa ya nemeta da aure wanda ita kuma ta ki yarda.

Wasu da dama na yiwa Adam Zango ganin mutum mai yawan auri-saki, bayan da ya rabu da matansa a karo na hudu, har da matarsa ta yanzu, wanda ya shelanta cewa suna daf da rubuwa, wanda a halin yanzu haka Safiyya na gidan iyayenta.

 

Sakamakon haka ne mutane ke ganin kai tsaye Lilin Baba ya nufi Adam A Zango ne da habaici, wanda ya ke nufin Allah ya tsallakar da Ummi Rahab, wanda da ace ta aure shi da yanzu Adam A Zango ita zai saka.

Subhanallahi Adam A. Zango ya saki matar sa saboda ta saka hoton ta a shafin TikTok Jarumi Adam A Zango ya saki matar sa Safiya Chalawa sakamakon saka hoton ta a manhajar TikTok

Jami’inmu na Labaranyau Blog ya samo rahoto cewa jarimin ya bayyana hakan ne a wani video a shafin sa na TikTok.

A cewar Zango, sai da ya gargade ta tun farkon auren su akan saka hotuna a social media.

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Watch African Stories

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button