Labaran Turanci

YANZU-YANZU: Kamfanin MTN Ta Rufe Ofisoshin Ta A Duk Faɗin Nąjeriya

Kamfanin MTN ya sanar da rufe dukkan ofisoshin sa dake Najeriya daga yau Talata 30 ga watan Yuli.

Wani jami’i na kamfanin MTN ne ya tabbatar da hakan ga jaridar TheCable har muka wallafo a Labaranyau..

Majiyar ta ce an ɗau matakin ne sakamakon farmakin da fusatattun mutanen da aka rufewa layuka suka kai wa kamfanin.

A ranar 27 ga watan Yuli ne dai ƴan Najeriya da dama suka kai kokensu bayan hana su amsa kira da yin kira a layukan nasu sakamakon rashin tantance lambar NIN dinsu.

A ranar Litinin ne wasu fusatattu masu amfani da layukan suka farmaki ofishin MTN dake Festac a jihar Legas.

Me zaka ce  angane da wannan mataki da Mtn ta  dauka na kulle ofisoshinta a duk fadin Najeriya?

Bada jimawa ba wani babban lauya ya maka Gwamnatin taraya a kotu dan gane wanda ya yanke diyar biliyan daya da rabi.

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Watch African Stories

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button