
Miyan Daddawa hadine da akeyi wa tuwo, ana iya cin miyar daddawa da kowani irin tuwo.
Dayawan mutane basu saka kayan hadin da yakamata shiyasa miyan daddawansu baya dadi wasu kuma basu bari miyan ya dahu dakyau.
Biyoni don samun ingantaccen tsarin yanda ake girka miyan daddawa.

Kayan Hadi
1. Daddawan kalwa
2. Attaruhu
3. Tattasai
4. Albasa
5. Tafarnuwa
6. Citta
7. Manja
8. Maggie
9. Gishiri
10. Bushasshen kifi
Yadda Ake Hada Miyan Daddawa
- Dafarko za a samu daddawan kalwa mai kyau
- Sai a daka daddawan kadan kar yayi laushi.
- A bare kifin a wankeshi da ruwan dumi da gishiri,
- A daura a kan wuta a sa mishi ruwa Rabin cup a barshi ya silala idan ya silala sai a sauke asa a gefe
- Sai a daura manja a soya shi da albasa.
- A wanke kayan miya a markada a zuba a cikin manjan a soya,
- A zuba dakkaken daddawan a yi ta soyawa har sai daddawan yayi kamshi sossai
- Sai a daka citta da tafarnuwa a ciki sai a juye kifin da dan ruwan jikin kifin duka a ciki tare da maggie da gishiri
- Sai a Dan rage wutan,a barshi na tsawon minti talatin ya nuna a hankali miya ya kammala.
Ana cinsa da tuwon gero ko dawa ko da Duk wanda ya samu.