Girke GirkeTrending Updates

Yadda Ake Hada Kilishi A Kasar Hausa

Yadda Ake Hada Kilishi A kasar Hausa

Kilishi nama ne mai dadin gaske da dandano mai santi, kilishi yana nan Fale fale ne wanda ake gasa namar a kan gaushi ko kuma Oven.

Kilishi wata nau’i ne na saraffa nama, irin su Dambun nama, Balangu, Tsire da sauransu duka nau’in sarrafa nama ne.

Kilishi yana zama a bushe Kuma baya baci sai ya dau lokaci mai nisa.

An san cewa ita kilishi nau’i ne na sarrafa nama a kasar hausa, Arewa cin kasar Najeriya.

Kilishi

Namar kilishi ta sanu a fadin kasar gaba daya har makota Jamhuriyar Nijar, kamaru, Sudan, Ghana da chadi da sauransu.

Ita kilishi an fi yin ta da namar saniya, amma wasu sukan yi da namar rago ko na rakumi.

Tun a shekarun baya da suka gabata Mun san cewa ba kowa ke iya hada kilishi ba in ba wanda yake aikin kwata, mafi yawan lokuta zaka ga mahauta ne masu hada kilishi.

Kar ku manta cewa babu wanda bare iya sarrafa Kilishi ba, Sai dai idan baka koya ba.

Zaki iya hada kilishi wa mijinki a gida in akwai namar.

Biyo mu a hankali dan ganin yadda ake hada Kilishi kokuma ziyarci shafinmu na Girke Girke don koyan wasu nau’in abinci.

Kilishi
Kilishi

Abubuwan Da Ake Amfani Dasu Wajen Hada Kilishi 

Kayan Hadi:

1. Tsokar nama (Rago, Saniya ko Rakumi)

2. Gishiri

3. Maggi

4. Garin Tafarnuwa

5. Garin citta

6. Garin barkono

7. Garin kuli kuli

8. Garin soyayyar gyada

9. Albasa

10. Zuma

11. Kanamfari da masoro

Kayan Aiki: 

Wuka

Faranti

Wankakken Taburi ko leda

Kananan kwanika na zuba kayan hadin

Yadda Ake Hada Kilishi
Yadda Ake Hada Kilishi

Yadda Ake Hadawa Dalla Dalla

  • Da Farko dai Zamu fara da yanka naman fale fale, a fere shi da kyau  da nutsuwa dan kar wani wuri yayi nama dayawa wani wurin yayi kadan.
  • A tabbata anyi kokari wajen daidaiTa fitar namar.
  • Sannan Sai a baza fale falen namar a faranti koh babban leda, Sai a shanya a rana dan ya bushe na kwanaki zuwa lokacin da aka tabbatar cewa ya bushe.
  • Wasu Suna amfani da oven dan busar da naman yayin da ake saka zafin oven din ya zamto madaidaici.
  • Idan namar ta gama bushewa Sai dauko kayan hadin wanda mafi yawa a nika ya zama gari.
  • Sai hadasu waje daya, a hada duka sinadarin a juya. A saka ruwa kadan kar yayi ruwa ruwa Kuma kar yayi kauri sosai.
  • A dauko bushashshiyar namar, Sai a shafa kayan hadin A jikin namar. A shafa gaba da baya, Sai a saka a rana ya bushe. In ya bushe Sai a watsa mai zuma kadan a jiki inda halin zuman kamin Sai gasa da gaushi dan kayan hadin ya shiga cikin namar da kyau.
  • In Kuma da Oven za ayi, Ana dauko bushashshiyar namar, a shafa kayan hadin yaji da kyau, Sai a saka a cikin oven a gasa. Kuma kar a manta a oven Ana sa karfin wutan kadan ne.

Ga Bidiyon Yanda Ake Hada Kilishi Cikin Sauki


Discover more from Labaran Yau

Subscribe to get the latest posts sent to your email.

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Discover more from Labaran Yau

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading