
Tuwon gero tuwo ne wanda aka samo asalinsa a kasar hausa, anfi yin sa da cin sa a arewacin Najeriya.
Biyomu dan samun bayani game da yadda ake girka tuwan gero.
Kayan Hadi
- Gero
Yadda Ake Hadawa
- Idan aka surfe a bushe sai a wanke
- A baza ya bushe sai akai nika idan an niko sai a tankade
- Sannan a daura ruwa a kan wuta idan ya tafasa sai ayi talge.
- Idan talgen ya tafasa sai a rage wuta ya na turara kadan kadan
- Sai a debo garin geron a zuba a kai yayi tozo
- A barshi yayi ta nuna a haka yakai kamar minti arba’in ko hamsin saboda shi Yana da wuyan nuna,kuma ba a rufewa kuma shi gero yana son wuta.
- Sai a tuke shi ya tuku sossai sai a Dan yayyafa ruwan zafi a fai a rufe a bar shi ya turara na tsawon minti talatin aman ba a sa ruwan sanyi haka ma idan za a yi tuwon dawa.
Ana ci da kowace irin miya, daga kan miyan kuka, kubewa, Miyar Taushe da sauransu.
Aci tuwo lafiya