
Ranar alhamis, 25 ga watan Yuli, shugaban Kasa Ahmed Bola Tinubu ya gayyaci Sarkin Musulmi da Ooni of Ife zuwa gidan gomnati domin tattauna wa akan zanga zanga da matasa ke shirin yi a 1 ga watan augusta.
Taron dai wani bangare ne na kokarin shiga tsakanin masu ruwa da tsaki da kuma kaucewa barkewar rikicin kamar yadda shugaban ya jaddada kudirinsa na bayyana sauye-sauyen tattalin arziki da kuma hasashen alfanun da al’ummar kasar ke samu.
Kamar yanda rahoto tazo Tinubu yayi nuni dacewa lallai bayida wani uzuri da zai iya bawa ‘yan kasa kan halin da taltalin arziki yasa kasa. Amma yana da qiyasin cewa komai zai iya dai daita bisa ga matakin da aka dauka.
A Fadin hakane ya kara da jaddada kokarin da gomanati keyi dan magance hakan. Yayi bayanin guntayen matakin da gomnati take dauka a yanzu haka.
Kuma ya dada da cewa a yanzu haka ma taltalin arzikin tanan farfadowa da kadan da kadan, hakuri za’ayi don yana kyakkyawan zato akan abin da Najeriya da ‘yan kasa zasu chimma in aka samu wannan nasaran.
Sannan akwai matakai, na gaggawa dakuma masu dogon zango dasuka fara tasiri wa taltalin arzikin wanda gomnati na kan kara dagewa wurin bullo da hanyoyin da zasu kawo mafita.