
Dan Wasan kwaikwayon Nollywood Yul Edochie ya rasa babban dansa
Shahararren dan wasan kwaikwayon Nollywood Yul Edochie ya rasa dansa ranan laraba. Wani na kusa dashi jarumin ya fadawa dailytrust cewa, dansa Kachichukwu ya fadi ne a yayin da yake wasa buga kwallo ya Kuma rasa ransa.
Bayan ya fadi, akayi wuff dashi zuwa asibiti a yayin da yake kwance ba hayacinsa ba. Bayan karamin lokaci aka tabbatar musu da cewa yaron ya rasu.
Marigayi kachichukwu ya cika shekara sha shida a watan junairu, wanda mahaifin nasa Yul Edochie yakai kan shafinsa na Instagram don murnan haihuwansa a wannan shekaran.