Girke GirkeLabaran Hausa

Yadda Ake Girka Miyar Waken Suya

Miyar waken suya miya ce meh inganci wanda aka fi ci a kudancin kasar najeriya.

Amma wahalarsa yasa mutane dayawa basu iya girkawa, a saukake ga yadda ake hada miyar waken suya (Soya Beans soup).

Kayan Hada Miyan Suya

1. Waken suya

2. Tumatur

3. Ataruhu

4. Albasa

5. Ganyen albasa

6. Maggi

7. Manja

8. Citta

9. Alayyahu

Miyar Waken Suya
Miyar Waken Suya

Yadda Ake Girka Miyar Waken Suya

  • A sami waken suyan a tsinceta a gyara.
  • Sai a jika kamar na minti 15 akai amarkada.
  • A sa kayan hadi.
  • Sai a soya manjan daga nan sai a zuba markadaden kayan miya
  • A rufe idan ya soyu sai a zuba wannan markaden waken suyan akai.
  • A rufe tukunyar na minti goma zuwa shabiyar
  • Sai a zuba ganyen na alayyahu da ganyen albasa.
  • A iya ci da tuwon semo, ko na gari ko tuwon shinkafa ko sakwara.

Wannan miyar tana da auki sosai.

Ga Bidiyon Yanda Ake Miyar Waken Suya


Discover more from Labaran Yau

Subscribe to get the latest posts sent to your email.

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Discover more from Labaran Yau

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading