
Wani jigo a jam’iyyar APC, Dr Abdallah Yakubu ya ce zaben Abdullahi Ganduje a matsayin shugaban jam’iyyar na kasa zai bayar da hanyar sulhu ta gaskiya.
Yakubu ya bayyana haka ne a Abuja, yayin da ya yabawa majalisar zartarwa ta kasa, NEC, na jam’iyyar bisa amincewa da Ganduje, tsohon gwamnan jihar Kano, bisa hangen nesa da hikima.
“Wannan zai baiwa jam’iyyar damar dagewa kan nasarar da ta samu bayan babban zaben 2023,” in ji shi.
Jigon jam’iyyar APC daga Adamawa wanda shi ne shugaban jam’iyyar ACN/AC United Kingdom da Ireland ta Arewa a lokacin, ya bayyana Ganduje a matsayin mutum na kwarai.
Yakubu ya lura cewa kishin Ganduje ga jam’iyyar musamman a lokacin zaben 2023 ya cancanci a kula da shi.

“Saboda haka, zabin Ganduje ya kasance bisa hikima da hangen nesa. Jam’iyyar ta fi mu duka kuma ta fi mu girma. Don haka ina so in taya sabon shugaban kasa murna.