Girke GirkeLabaran Hausa

Yadda Ake Girka Soyayyen Kabeji (Fried Cabbage)

Ita Soyayyar Kabeji hadi ne zamani dan gyara nau’in abincin mu, ita kabejin da aka soya ana iya cin shi da shinkafa Jollof ko Fried, Ana iya ci da couscous ko taliya ko macaroni, da sauransu.

Biyoni domin samun cikakken bayanin yanda ake girka soyayyen kabeji.

Kayan Hada Soyayyen Kabeji

1. Kabeji

2. Kwai

3. Mangyada

4. Maggie attaruhu

5. Albasa

6. Maggi

7. Gishiri

Soyayyan Kabeji
Soyayyan Kabeji

Yadda Ake Girka Soyayyen Kabeji

  • Da farkon za’a wanke albasa da kabeji a tsantsame
  • Sai a yanka a daura man gyada a wuta.
  • A sa albasa a soya idan ya soyu sai a zuba kabeji a ciki sannan sai a rufe
  • Bayan minti uku haka zuwa biyar sai a bude za a ga ya danyi ruwa,
  • Sai a kada kwai a saka attaruhu, albasa, Maggie da gishiri idan anaso aman idan ba a so ba sai an sa ba
  • Sai a zuba a Kai ana soyawa ana juyawa har ya soyu sai a juye a kwano aci shinkafa ko taliya ko dan wake ko couscous.

Aci Dadi lafiya


Discover more from Labaran Yau

Subscribe to get the latest posts sent to your email.

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Discover more from Labaran Yau

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading