
Laporte Ya Sanar Da Tafiyar Sa Daga Man City Zuwa Saudi
Dan wasan tsaron gida na Manchester City “Aymeric Laporte“ ya sanar da zai bar Man city ne a wani video a social media.

Laporte ya sanar da amincewar sa na komawa Al-Nassr bayan shekara biyar da rabi dayayi a England.

Dan kwallon kafa na kasar Spain din “Aymeric Laporte” zai zama sabon kwararren dan kwallon kafa daya yarda zai buga kwallo a kungiyar kwallon kafa na “Saudi Pro League” bayan dan wasan da suka buga kwallo a Man city tare “Riyad Mahrez” daya koma Al-Ahli a watan daya wuce.