Cikakken Tarihin Ibrahim Traore
Shafin labaranyau.com ta kawo muku cikakken bayani da tarihi kan shugaban kasar Burkina Faso mai suna Ibrahim Traore.
Rayuwar Ibrahim Traore
Ibrahim Traore wanda aka haifa a garin Kera, Bondokuy, mouhoun kasar Burkina faso a shekarar 1988, soja ne kuma ya kasance shugaban kasa ko mai rikon kwaryar shugaban kasa na Burkina faso. Bayan sun karbi mulki daga hannun tsohon shugaban kasar Paul-Henri Sandaogo Damiba. Traore na da shekara 34 hakan yasa ya kasance shugaban kasa mai karamin shekaru a duniya.
Karatun Ibrahim Traore
Traore yayi karatun firamare a garin bondokuy, sai ya wuce Bobo-Dioulasso inda yayi karatun sakandare. Ya kasance bai surutu ba kuma mutum ne mai fikira. A shekarar 2006 ya karanta Geograpy a jami’ar Ouagadougou inda ya samu digirinsa na farko. Yana cikin kungiyar musulmai na dalibai da kungiyar Marxist. An San Ibrahim da tare fada wa yan ajinsu in aka samu tangarda. Ya kammala jami’ar da sakamako mai kyau.
Aikin Sojan Ibrahim Traore
A shekarar 2009 Traore ya shiga aikin soja na kasar Burkina Faso inda ya samu horaswa a makarantar horaswa na soja Georges-Namoano. An tura shi na anti aircraft a kasar Moroko kamin aka tura shi fannin infantry a garin kaya na arewacin burkina faso.
Ya samu karin girma zuwa lieutenant a shekarar 2014, kuma Yana daga cikin sojin da Majalisan dinkin duniya ta tura Mali dan kawo zaman lafiya mai taken MINUSMA.
Ya nuna jajircewa da aiki tukuru wajen yaki da yan ta’adda a timbuktu. Sannan ya dawo Burkina faso a lokacin da yan ta’adda suka ta’addanci. Ibrahim yayi yaki a Djibo da kuma arewacin kasar dan kawo karshen yan ta’adda a 2019.
Ya samu karin girma zuwa Captain a shekarar 2020. Traore ya bayyana rudewansa Saboda rashin makamai na sojan kasar kuma yan siyasa suna cika jaka da kudaden cin hanci da rashawa.
Ya zamo mai magana da yawun sojin arewacin wanda suke jin haushin gwamnati na rashin yin abin da ya dace.
Juyin Mulkin Ibrahim Traore
Traore Yana daga cikin sojin da suka mara baya wajen yin juyin mulkin watan junairu na shekarar 2022. Daga watan maris ya zamo shugaban gidan kayan yaki na kaya.
Mafi yawan mutanen da suke goyon bayan juyin mulkin basu jin dadin sabuwar gwamnatin soja Saboda Paul-Henri Sandaogo Damiba baya musu abin da suke so kuma suka tsara. Ta inda suka kasa kawo karshen ta’addanci a kasar. Traore ya bayyana cewa shi da wasu sojin sunyi kokari dawo dashi shugaban kan hanya Amma giyar mulki ta dibe shi.
Rashin jindadin yafi yawa cikin kananan sojin kasar wanda ke fuskantar yan ta’addan a fagen yaki. Kuma Ana samun delay wajen biyan Sojin Cobra.
A yayin da masu juyin mulki suka yi juyin mulki ran 30 ga watan satumba Traore Yana matsayin sa na captain, anyi juyin mulkin da goyon bayan Cobra. Amma kuwa Traore yasan duk yadda akayi ya karbi mulkin duk da babu hannun shi ciki. Nan ya bayyana shine sabon shugaban kungiyar Patriotic Movement for Safeguard and Restoration ranar 6 ga watan Oktoba. Ya zamo shugaban kasar kuma yayi alkawarin za’ayi zabe dan komawa mulkin demokradiyya a watan juli shekarar 2024.
Aikin Ibrahim Traore A Matsayin Shugaban Kasa
Bayan Ibrahim Traore ya zabi Prime Minister Kyélem de Tambela, abin da suka fara shine rage albashinsu da na ministoti, a cewar sa Burkina Faso barata samu cigaba ba in sun fita layin Thomas Sankara.
Tsohon shugaban kasar Paul-Henri Sandaogo Damiba ya Kara nashi albashin ne bayan zama shugaban kasa dashi da ministoci. Shugaban kasa Ibrahim Traore yaki karban albashin shugaban kasa, inda yake karbar albashin sa na captain na soja domin ya nuna wa kasar cewa Yana aiki ne da kishin kasa ba don san kai ba. Saboda halin da ake ciki a kasar.
A watan nowamba ministocin sun bada rabin albashin su wa gidauniyar taimakawa marasa galihu da kutare da makafi domin inganta rayuwar su.