Cikakken Tarihin Bala Abdulkadir Muhammad Kauran Bauchi
Labaranyau.com ta kawo muku cikakken tarihin Sanata Bala A. Muhammed tare da bayani a saukake kan Siyasar sa, aikinsa, karatun sa Iyalen sa da sauransu.
Rayuwar Bala Muhammad
Bala Abdulkadir Muhammed shine asalin sunan kauran Bauchi, an haifeshi ranar 5 ga watan Oktoba 1958 a garin duguri wanda ke karamar hukumar Alkaleri na jihar Bauchi. Kaura dan Siyasar najeriya ne.
Karatun Bala Muhammed
Kaura yayi karatun firamare a firamaren gwamnati na garin duguri, daga 1965 zuwa 1971 inda ya samu takardan kammala firamare (FSLC). Daga nan ya wuce Sakandaren gwamnati na Bauchi daga shekarar 1972 zuwa 1976 inda ya kammala da WAEC.
Sai ya ja gaba da karatu a Northeast Kwalajin Art da science daga 1977 zuwa 1979 inda yayi Advanced level certificate. Daga nan ya samu admission a jami’ar maiduguri a 1979 inda ya kammala digirinsa a Fannin Turanci a shekarar 1982.
Kaura ya samu horaswa a Administrative staff college of Nigeria (ASCON) a shekarar 1988 kan general management. Ya kuma samu horaswa kan capacity building a legas inda ya kammala da certificate of the Institute of Purchase & Supplies a shekarar 1997.
Aikin Bala Muhammed
Yafara aikin jarida inda ya taka matakala har yakai matsayin News Editor a gidan jaridar mirage ta garin Jos tsakanin 1982 zuwa 1983. Ya kuma yi aiki a matsayin mai rahoton labarai wa News Agency of Nigeria, na ya wuce ya koma aiki a gidan jaridar democrat inda yayi aiki a matsayin Editan jihar Benue daga 1983 zuwa 1984. A nan ya bar aikin jarida inda ya samu aiki da federal ministry of Internal affairs a matsayin Administrative officer a Abuja.
A shekarar 1994 ya samu karin girma zuwa matsayin Principal Officer a Cabinet secretariat na fadar shugaban kasa.
Ya zama chief supply officer a federal ministry of solid minerals daga shekarar 1995 zuwa 1997, inda ya kai matsayin Mataimakin darakta a federal ministry of power and steel a shekarar 1997, zuwa 1999 ya rike muqamin deputy darakta kuma SA na ministan transport, yayi aiki har zuwa 2003.
Siyasar Bala Muhammed
Kaura yayi ciyaman na karamar hukumar Alkaleri zuwa shekarar 2007. Ya kuma lashe zaben Sanata a shekarar 2007 inda ya jagoranci mazabar Bauchi ta kudu a Majalisan dattawa, kuma yayi aikin duba a kwamiti daban daban na Majalisan wanda sun hada da: kwamitin Solid Minerals Development; rubuta tsare tsare (brochure),Ministry of Solid mineral development; Panel on Cabotage Laws, Federal Ministry of Transport; presidential committee on charges, tariffs and duties in the marine industry; kwamitin Inland Container Terminals; Member, Ministerial Delegation to Russia, UK, Liberia, Brazil and Turkey on Nigerian’s nominee for Secretary General, kwamitin International Maritime Organisation (IMO); Mamba na kwanitin International Maritime Organisation Congress da sauransu.
Kaura ya kasance jajircaccen wakili ne wanda ya yi gwagwarmaya dan cigaban najeriya. Bayan rasuwar Tsohon shugaban kasa Yaradua, ya dage domin a bi dokar daura Goodluck Jonathan a matsayin shugaban kasa wanda hakan ta kai da Goodluck ya bashi ministan Birnin tarayya Abuja.
Yayi takarar gwamna a Bauchi a shekarar 2019 inda ya lashe zaben ya doke gwamna mai ci na jam’iyar APC Barista MA Abubakar da kuri’u 515,113.
Ya kara takara a jam’iyar PDP a shekarar 2023 inda ya lashe zaben ya doke Airmarshal Sadeeq Abubakar na jam’iyar APC.
Iyalen Bala Muhammed
Sanata bala kauran Bauchi ya kasance musulmi kuma Yana da mata sama da daya da kuma yara masu yawa wanda sun hada da shamsu, zarah, dullas da sauransu.
Hotunan Bala Muhammed