Cikakken Tarihin Shehu Sani
Shafin labaranyau.com ta kawo muku cikakken tarihin Sanata Shehu Sani.
Rayuwar Shehu Sani
Shehu Sani Tsohon dan gwagwarmayan neman yancin mutane ta fannin siyasa wanda yayi sanadiyar kulle shi a kurkuku da hukuncin dauri har tsawon rayuwar sa a mulkin soja kuma dan siyasa ne, kwamred tsohon Sanata ne na Majalisan dattawa ta jihar kaduna ta tsakiya. An haife shi a jihar kaduna, ran 29 ga watan Oktoba shekarar 1967.
Karatun Shehu Sani
Shehu ya yi karatun firamare a makarantar firamare ta badarawa ta kaduna, inda ya samu takardan kammala firamare a shekarar 1980. Nan take ya wuce ya cigaba da karatun sakandare a kwalajin fasaha ta gwamnati Kagara a jihar neja. Ya kuma shiga Polytechnic inda ya kammala da takardan HND a shekarar 1993.
Aikin Shehu Sani
Sani Mawallafi ne kuma marubuci ne wanda ya yi gwagwarmaya dan samun yanci na demokradiyya da kuma yancin yan kasa. Shine shugaban kungiyar gwagwarmayan yancin jama’a Civil Right Congress of Nigeria. Da kuma ciyaman na Hand in hand Africa.
A matsayin sa na dan gwagwarmayan yancin demokradiyya a lokacin mulkin soji, an kulle Kwamred a lokuta daban daban Saboda jajircewa kan dawo da mulkin demokradiyya a najeriya.
An tsare na rayuwa a fursuna lokacin mulkin Janar Sani Abacha, Amma an sake shi bayan an koma mulkin demokradiyya a shekarar 1999.
Siyasar Shehu Sani
A zaben 2015, yayi takara kuma ya lashe zaben kujerar sanata na jihar kaduna ta tsakiya a jam’iyar APC.
Shehu Sani mamba yayi mamba na wasu kwamiti a Majalisan dattawa wanda sun hada da kwamitin bashin cikin gida da waje, kwamitin duba kan dokoki da mu’amalar waje.
Yayi aiki tukuru kan mu’amalar kasashen waje da kuma akan ilimi.
Iyalen Shehu Sani
Sanata Shehu Sani Yana da aure da kuma Allah ya albarkace shi da yara.
Karramawan Shehu Sani
Shehu Sani ya samu karramawa Daga wajaje daban daban kamar su kungiyar marubutun turanci na Jami’ar Ahmadu Bello na Zaria. Ya samu karramawa na digiri daga Institute of Continuous Education.
Ya samu karramawa na shiga shahararre (hall of fame) na kungiyar mawallafa na najeriya.
Ya samu karramawa na “Gwarzon Demokradiyya” daga Tell magazine.
Sani ya samu karramawa National Conscience Party, da Swedish based Iqbal Masih for the Right of the Child, ya samu karramawa na ambasada na zaman lafiya daga International Peace Foundation, da kuma karramawa Arewa Youth Foundation.
Shafin Sadarwan Shehu Sani
Shehu Sani a Facebook
Shehu Sani a Twitter Yanzu X
Shehu Sani a Instagram
Da kuma shafin sa na yanan gizo.
Arzikin Shehu Sani
Arzikin Shehu Sani ya kasance Yana boye domin bai bayyana ba. Amma labaranyau.com tana aiki tukuru domin hado arzikin sa da kuma hanyar samun kudinsa bayan ya bar kujerar sanata.