Labaran Hausa

BAUCHI: Gwamna Bala Ya Kaddamar Da Aikin Sabunta Majalisar Dokoki ta Jiha Kan Kudi Naira Biliyan 7.8

Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed, ya kaddamar da aikin sabunta, sake fasalin da kuma inganta ginin majalisar dokokin jihar Bauchi, wanda darajar aikin ta kai Naira biliyan 7.8.

Da yake jawabi yayin bikin kaddamar da aikin a ranar Talata, gwamnan ya bayyana cewa wannan aiki yana nuna kudirin gwamnatinsa na samar da ingantaccen yanayi ga dukkan rassan gwamnati a jihar.

A cewarsa: “Sabuntawa, sake fasalin da kuma inganta ginin da muke shaida yau yana nuni da adalci da daidaito ga dukkan rassan gwamnati guda uku da ke zaman ginshiƙai na tafiyar da gwamnati.”

Governor Bala Mohammed
Governor Bala Mohammed

Gwamna Bala ya jaddada muhimmancin gyara ginin majalisar domin ya dace da matsayin da take da shi a tsarin mulki da shugabanci, tare da tanadin kayan aiki da suka dace.

Ya kara da cewa: “An kaddamar da wannan aiki a kan kudi Naira biliyan 7.8, inda aka riga aka biya kashi 50 cikin dari na kudin ga kwangilar. Ana sa ran za a kammala aikin cikin watanni 12.”

Gwamnan ya bayyana cewa hadin kai da fahimta tsakanin bangaren zartarwa da na majalisa ne ya ba da damar gudanar da ayyukan raya kasa cikin sauki da inganci.

A nasa jawabin, Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Bauchi, Rt. Hon. Abubakar Y. Suleiman, ya bayyana cewa ginin majalisar ya samo asali ne tun zamanin jamhuriya ta farko a shekarun 1980 a karkashin marigayi Gwamna Abubakar Tatari Ali.

Ya ce banda karamin gyara da aka yi a shekarar 2011, babu wani babban gyara da aka taba yi wa ginin.

Ya bayyana cewa ginin ya dade yana kasancewa cibiyar ayyukan dokoki na jihar, kuma lokaci ya yi da ya kamata a gyara shi yadda ya dace.

Ya ce: “A madadin dukkan ‘yan majalisar dokoki ta jihar Bauchi, ma’aikatan gudanarwa da sauran ma’aikata, muna mika godiyarmu ga Gwamna Bala saboda hangen nesansa da jajircewarsa wajen bunkasa gine-ginen majalisa da na sauran sassan jihar baki daya.”

“Wannan gyara ba wai kawai sabunta gini ba ne, illa ma ya nuna sabuwar alwashin gaskiya, inganci da isar da ayyuka ga jama’a.”

Ya bayyana cewa aikin zai kawo sauyi ta hanyar zamani, ya inganta yanayin aiki da kuma bai wa majalisar damar sauke nauyin kundin tsarin mulki da isar da ayyuka ga jama’a yadda ya kamata.

Kakakin ya bukaci ‘yan majalisa, ma’aikata da al’umma gaba ɗaya da su dauki aikin a matsayin amanar gama-kai da ci gaba da karfafa dimokuradiyya da shugabanci nagari, tare da kafa tarihi mai dorewa ga al’ummar jihar.

Shi ma da yake jawabi, Kwamishinan Gidaje da Muhalli, Danlami Ahmed Kaule, ya tabbatar wa jama’a cewa ma’aikatarsa za ta sa ido sosai domin tabbatar da cewa aikin zai kasance mai inganci da kammaluwa cikin lokaci.


Discover more from Labaran Yau

Subscribe to get the latest posts sent to your email.

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Discover more from Labaran Yau

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading