
Suwaye Suka Kai Hari Jirgin Qasa Abuja Kaduna – Bukarti
Masana da masu nazari kan harkokin tsaro a Yammacin Afirka sun bayyana cewa da alama ‘yan kungiyar Ansaru, wacce ke ikirarin kishin Musulunci, ne suka kai hari kan jirgin qasan da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna a watan jiya.
A ranar Laraba ne, wani bidiyo da aka fitar ya nuna wasu daga cikin maharan dauke da bindigogi suna iƙirarin cewa su ne suka sace fasinjojin jirgin ƙasan a ranar Litinin din makon jiya.
Bidiyon, wanda bai kai tsawon minti 1:30 ba, ya nuna hudu cikin ‘yan bindigar sanye da kakin sojoji fuskokinsu a rufe a tsaye suna ikirarin ci gaba da riƙe fasinjojin jirgin qasa da suka sace a karshen watan jiya.
Ba a ga fasinjojin a cikin taqaitaccen bidiyon ba, amma mutanen da suka yi maganar sun tabbatar da cewa suna riqe da su.
Discover more from Labaran Yau
Subscribe to get the latest posts sent to your email.