
Dalilan Da Yasa Na Saki Fati Muhammad – Mai Iska
Tsohon Jarumin masana’antar Kannywood kuma tsohon mijin Jaruma a masanantar Fati Muhammad, Sani Musa Mai Iska yayi karin haske kan dalilin mazge aurensa da jarumar.
Sani wanda ya bayyana lamarin a matsayin kaddarar aure da ka iya afkuwa a duk lokacin da ubangiji ya tsara. Ya ce maksudin abinda ya kawo rabuwar aurensu da Fati shine “ta saka soyayyar mahaifiyarta a gaba yayin da shi kuma ya saka na karatunsa a gaba.” kamar yadda ya wallafa a shafinsa ta Facebook.
Mai Iska ya kara da cewa saki biyu kacal yayi mata amma ta bayyana wa Duniya cewa saki Uku yayi.
Mu tuna a baya cewa, Yan watanni kadan bayan bikin nasu suka tafi Kasar Ingila sakamakon samun damar shiga wani shiri na wayar da kai kan Kanjamau da ita jarumar ke yi a Kasar.