Girke GirkeLabaran Hausa

Yadda Ake Fruit Salad Na Custard Da Madara

Ana yin fruit salad iri iri, yau Mun kawo muku wata nau’i na fruit salad wanda ake yi da custard da madara.

Biyomu kadan jin takaicaccen bayani game sarrafa wannan salad mai Dadi.

Kayan Hada Fruit Salad Na Custard Da Madara

1. Lemo

2. Apple

3. Ayaba

4. Inibi

5. kankana

Duk Wanda ka samu kaman guda biyar ko fiye

6. Madara

7. Zuma ko sugar

Fruit Salad Na Custard
Fruit Salad Na Custard

Yadda Ake Hada Fruit Salad Na Custard Da Madara

  • Dafarko zaa zuba madara da ruwa a kwano a gauraya kaurin dan daidai ba tsalalo ba
  • Sa’annan a zuba a tukunya ana juyawa ya tafasa
  • Bayan ya tafasa sai asaka garin custard a kwano asa ruwa a gauraya shima kar yayi kauri kuma kar yayi tsalalo
  • Sai a juye a madaran dake tafasan ana juyawa custard din ba mai yawa ba saboda baaso yayi kauri kaman kunu
  • Sai a saka zuma ko sugar abarshi yadan huce
  • Sai a yayyanka fruits din a kwanon da zaa hada
  • Sa’annan a juye wannan madaran custard da aka hada akai  a dan jujjuya
  • Sai a saka zuma akai.

Custard ya kammala sai a deba asha.

Ga Bidiyon Yanda Ake Custard

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Watch African Stories

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button