
DSS na kara wa wuta gaushi: ‘Yan Najeriya na shirin gabatar da kara a ranar 1 ga watan Agusta domin nuna adawa da wahalhalun da suke fuskanta a karkashin gwamnatin shugaba Bola Tinubu.
Wani mai fafutuka, Omoyele Sowore a ranar Litinin ya ce hukumar tsaro ta farin kaya, DSS, tana gudanar da gagarumin aiki wajen zaburar da ‘yan Najeriya domin gudanar da zanga-zangar ta #EndBadGovernanceInNigeria a ranar 1 ga watan Agusta.
Sowore yana maida martani ne kan matakin da hukumar DSS ta dauka na tsare daya daga cikin masu gangamin zanga-zangar ranar 1 ga watan Agusta da aka fi sani da @Mallam_jabeer.
Wani mai amfani da X(Twitter) mai handle @n6oflife6 ya posting kamar haka:
“Na samu kira daga @Mallam_jabeer cewa hukumar DSS ta tsare shi. Wannan matashin mai zaman lafiya ne kuma ya kasance mai bin doka da oda kan shirye-shiryen zanga-zangar da ya yi.
“Kama shi kafin ranar 1 ga Agusta ba shi da ma’ana. Ana kokarin ganin an sako shi. Najeriya mun gode muku.”
Omeyele Sowore, da yake mayar da martani, ya rubuta:
“Hukumar @OfficialDSSNG tana yin aiki mai ban sha’awa don tayar da #EndBadGovernanceInNigeria tawaye. #FreeJabirNow.”