Labaran YauNEWSTrending Updates

ATBU Ta Yi Tsokacin Bill Na Miliyan ₦61 Na Wutan Lantarki

Jami'an Atbu na tarayya ta yi korafi bisa ga yawan kudin da hukumar wutan lantarki take chazanta a wata

A makon daya gabata ne hukuman lantarki na Nepa takai wa Jami’an ATBU Bauchi lissafin bill na Miliyan ₦61. Hakan Ya jayo tirjiya da tsokaci daga kunguyar Jami’an tarayya.

Sabon shugaban jami’an me suna Professor Sani Usman Kunya, wanda ya karbi ofis din shugaban ATBU a watan April 19, 2024, yayi tsokacin yawan kudin bill din da nepa ta kawo.

Yace lallai wannan lissafi da sakel, wutan lantarkin da Nepa ke bawa Jami’an be kamat yakai wannan lissafin ba. Hakan ya jawo tsai da wutan lantarki na awanni 24 zuwa ATBU.

Zaman Gaggawa Na Kungiyar Jami’an ATBU

Lamarin ya jawo zaman gaggawa na kungiyar jami’an ATBU, wanda sun shafe awanni wurin tattaunawa akan lamari mai abun mamaki.

Cikin gaggawa aka samu dai datuwa tsakaninsu yanda har suka cire hanya mai tasiri dan shawon kan matsalan. Kungiyan wutan lantarkin sun karbi hukuncin da kungiyar Jami’an ta yanke.

Babu jimawa aka samu sulhu har wuta ya dawo cikin gaggawa. Amma wakilin Nepan ya tabbatar da cewa wutan lantarkin da suke tura wa jami’an ya ban banta da wurare da yawa a cikin garin.

Hakan ya fito fili yayin tattaunawa da wasu dalibai dake zama a dakin kwanan dalibai na makarantar, wanda suka tabbatar da irin samun wutan da akeyi ya wadata.

Sannan sun kara da nuna tasirin da wutan ke dashi a gurin dalibai, sunce samun wutan na taimaka musu wurin samun ingantacciyar daman yin karatu cikin sauki da dadi.

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Watch African Stories

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button