
Sunanta Hafiza Aindati: Jarumar Senegal da Ta Dauki Duniya da Karatun Al-Qur’ani
Wata gagarumar nasara ce ta zo daga Senegal, inda Hafiza Aindati, wata baiwar Allah daga kasar, ta lashe gasar karatun Al-Qur’ani na mata karo na 60 da aka gudanar a Dubai.
Abin da ya fi daukar hankalina ba wai nasarar ba ce kawai, amma irin yadda al’ummar Senegal suka tarbe ta da farin ciki da alfahari.
Rali, aka Shirya, mutane suka fito kafafu don nuna soyayya da girmamawa ga wannan jaruma mai rikon Al-Qur’ani.
Wannan ya nuna mana yadda Al-Qur’ani Maigirma ke da matsayi mai girma a kasar Senegal, da yadda suke karrama masu haddace shi da kuma bin tafarkin sa.
A gaskiya, irin wannan karbuwa da mutuntaka da aka nuna wa Hafiza Aindati wata tambaya ce gare mu: Mu fa? Shin muna karrama ma’abota Al-Qur’ani irin haka?
Kukan Zuciya:
“Yaa Allah, Ka kara mana kaunar LittafinKa Mai Tsarki. Ka sa mu kasance daga cikin wadanda za su samu ceto ta sanadin Al-Qur’ani ranar da babu ceto sai naka. Ameen.”


Al-Hassan Aliyu Miqdad | Nigeria 27th Gasar Kasa da Kasa ta Dubai
Discover more from Labaran Yau
Subscribe to get the latest posts sent to your email.