Onana Ya Zama Dan Manchester United
A shekaran jiya ne kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta kammala daukan andre onana. Mai tsaron ragar dan kasar kamaru ya rattaba hannu akan kwantaraginsa na shekara biyar da kuma zabin kara shekara daya.
Dan wasan dan shekara ashirin da bakwai ya gana da manema labarai a karon farko kafin ya hau jirgi ya tafi amerika inda yan wasan Manchester United din ke atisayensu.
A hirar tasa yace “ina matukar farin cikin samun wannan dama na zama daya daga cikin wannan baban kungiya, ina alfahari sosai”.
Ya kara da cewa Manchester United tana daya daga cikin manyan kungiyoyin kwallon kafa a duniya, ina da abokai da suka buga a wannan kulob da kuma Edwin Van der Sar lokacin da nake kwallo a Ajax.
Sannan ya kara da cewa “Iyalai na suna alfahari kuma nima ina murna. Abun alfahari ne a kasata kamaru da nahiya ta afrika ace ina bugawa a wannan kungiya”.
Sannan yace zaiyi iya kokarinsa domin dawo da martabar wannan kungiya ta Manchester United a idon duniya.