FootballLabaran YauTrending Updates

Guardiola Ya Fara Ganin Duhu A Gasar Premier – Arteta Ya Gano Lagon Mancity

Pep Guardiola tabbas ya ji kamar yana cikin mafarki mai maimaitawa yayin da yake kallon yadda Manchester City ke kokarin karya Arsenal a karo na biyu.

Arsenal wadda ta rage yan wasa zuwa 10 a minti na 45 da korar Trossard da akayi, ta shafe kusan rabin na biyu ne da ‘yan wasan baya biyar da ‘yan wasan tsakiya hudu, wani lokacin ma kasa da yadi 2, wanda hakan ya hana City hari a gefen bugun fanareti.

Tsayawan daka na minti 45 a irin wannan kungiyar mai ban tsoro kamar City na iya zama kamar aikin da ba zai taba yiwuwa ba ga Arsenal.

Amma sun kusa cire ma City kwadayi, kuma Guardiola yana da laifi yadda ‘yan wasansa suka yi ta gwagwarmayar na yin nasara, sai da Stones ya kawo dauki da saka kwallo da kayi a karshe.

 

Idan har har yanzu akwai wanda ke da shakku kan mahimmancin Rodri ga Manchester City to ya daina, raunin da dan wasan ya samu a farkon rabin lokaci har ya tilasta masa fita daga wasan, hakan kawai ya nuna dalilin da ya sa shi ne dan wasa daya da Guardiola ba zai iya zama babu ba.

Rodri ya bayyana yana fama da rauni a gwiwarsa a wani karo da sukayi da Thomas Partey a mintuna 20.

An yi masa dogon jinya a filin wasa kafin Mateo Kovacic ya maye gurbinsa lokacin da aka bayyana cewa dan wasan tsakiya na Spain ba zai iya ci gaba ba.

Ba tare da Rodri ba, City ba ta da gam da ke riƙe ƙungiyar tare. Shi ne dan wasan tsakiya na duniya mafi kyawun mai tsaron gida, amma yana da sauran sinadaran kwallon fiye da haka, kuma basiran ƙirƙiran shi ne ya sa ya zama mai mahimmanci ga ƙungiyar.

City ba ta yi rashin nasara a wasan Premier da Rodri ba tun bayan da ta sha kashi a hannun Tottenham a 2023, wanda yanzu ya kai wasanni 52.

Dabarar da City ta yi ta kai ga masu tsaron baya Walker da Rúben Dias da Manuel Akanji suka bubbuga shot a  daga wajen filin tsaron gida, a fili ya nuna cewa Guardiola yakamata yayi wani abu.

Ya jira har zuwa minti na 70, kafin ya yi canjin Phil Foden wa Doku da sauran mintuna takwas kafin ya jefa Stones da Jack Grealish a cikin fafatawar.

Canje-canjen ba su da bambanci har sai da Stones ya zura, amma yakamata Guardiola ya girgiza wasan tun da farko.

Ba ya bukatar tsaka-tsaki biyu a filin wasa da kungiyar Arsenal ba tare da dan wasan gaba ba, kuma ya dauki lokaci mai tsawo kafin ya gabatar da Grealish.

A wannan karon City da Guardiola sun yi sha da kyar, amma Arsenal ta yi kusa yin kacakaca a bacin rai ga zakarun nayin nasara mai ban mamaki.

Amma Stones ya bar ɗanɗano mai tsami ga harshen Arteta, amma zai yi alfahari da yadda ƙungiyarsa ta kare gida na tsawon lokaci.

Sun fuskanci shot 20 a zagayena biyu, wanda Arsenal din ta kasa buga ko shot daya musamman a ƙarshen mako mai tsawo wanda ya fara da nasara.

A Spurs kuma zai ci gaba da wasan daren Alhamis a gasar zakarun Turai a Atalanta. Jiran nasara a City ya ci gaba, amma Guardiola ya san yana da babban abokin hamayyar da ke zaune kusa da madubin kallonsa.

Man City ba za ta iya cewa ba a gargade su ba ta kowace fuska. Jim kadan kafin Gabriel ya farke kwallon a minti na 45 wanda ya kusa zama kwallon lashe wasan.

Amma Stones ya farke a bugu daga baya, bayan haka kuma shi mai tsaron gida na Brazil ya saka samu irin wannan damar daga wani bugun da Saka ya yi.

Guardiola Ya Fara Ganin Duhu A Gasar Premier

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Watch African Stories

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button