NEWSLabaran Yau

Me Kukasani Game Da Sabon Shugaban APC? Abdullahi Adamu

Me Kukasani Game Da Sabon Shugaban APC?

Wanene Abdullahi Adamu?

Abdullahi Adamu yanzu haka shi ne Sanatan da ke wakiltar Nasarawa ta Arewa a majalisar dattawan Najeriya kuma sau biyu yana zama gwamna a jihar ta Nasarawa.

DOWNLOAD ZIP/MP3

Ya rike mukamin gwamnan jihar Nasarawa ne daga sekarar 1999 zuwa 2007. Hasalima shi ne gwamnan farar-hula na farko a jihar bayan dawowan demokaradiyya.

An haife shi a a 23 Ga watar yuli shekarar 1956 a garin Keffi da ke jihar Nasarawa kuma ya yi karatunsa na firamare da Sakandare a jihar Nasarawa da kuma Benue ta yanzu a daga 1960 zuwa 1962.

Ya kuma yi karatun gaba da Sakandare a Kwalejin Fasaha, Bukuru, da kuma Kwalejin Fasaha da ke Kaduna wato Kaduna state Polytechnic inda ya samu Babbar Difiloma.

A shekarar 1992, ya kammala Digirinsa na farko a fannin Lauya a Jami’ar Jos kuma ya zama lauya a 1993.

Sanata Adamu ya soma siyasa a 1977, kuma ya rike mukamai da dama.

Sanata Adamu ibrahim ya zama sabon shugaban APC ne fiye da shekara guda bayan sauke tsohon gwamnan jihar Edo Adams Oshiomhole daga mukamin da kuma nada Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe a matsayin shugaban kwamitin riko na jam’iyyar na tsawon lokaci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button