Biography

Chikekken Tarihin Dikko Umar Radda, Rayuwarsa, Dukiyarsa, Aikinsa, Iyalinsa, Siyasarsa Da Karatunsa

Chikekken Tarihin Dikko Umar Radda

Labaranyau.com ta kawo cikakken tarihin rayuwa, karatu, aiki, iyali da siyasar Dikko Umar Radda.

Dikko Radda shine gwamnan katsina tun bayan lashe zabe da yayi a zaben da ta gabata na zaben gwamnoni da akayi a shekarar 2023.

An haifi Dikko Radda ran 10 ga watan satumba a shekarar 1969, haifaffen dan jihar katsina, Musulunci shine addininsa. Yayi karatun sa a jamiar Ahmadu Bello da ke Zaria, ya kware a fannin tattalin arziki da kuma siyasa. Dan jam’iyar APC ne.

Chikekken Tarihin Dikko Umar Radda
Chikekken Tarihin Dikko Umar Radda

Asalin Dikko Radda

Asalin Dikko Radda
Asalin Dikko Radda

Umar Dikko Radda bafulatanin ne wanda aka haifeshi a Garin Hayin Gada. Asalinsa shi dan Karamar Hukumar Dutsin-ma na jihar katsina, An haifi Dikko Radda ran 10 ga watan satumba a shekarar 1969.

Karatun Dikko Radda

Karatun Dikko Radda
Karatun Dikko Radda

Dikko ya fara karatunsa na firamari a Radda Primary School daga shekarar 1974 zuwa 1980. Sai ya tafi zaria inda ya cigaba da karatun sakandare a Zaria Teachers College. Makarantar horaswa na malamai.

Ya samu takardar koyaswa wato NCE Certificate a kwalajin ilimi na kafanchan(Kafanchan college of Education) a shekarar 1986 zuwa 1990.

Radda ya wuce Jami’ar  Tafawa Balewa  a jihar Bauchi inda ya karanta tattalin arzikin noma (Agric.Economics and Extension), daga shekarar 1992 zuwa 1996 inda ya kammala digirinsa ta farko.

Daga shekarar 1998 zuwa 2004, yayi digiri Ta biyu a jami’ar Ahmadu Bello inda ya kammala da MSc Agric Extension and Rural Sociology.  A shekarar 2005 ya kammala Masters a kan harkar Muamalan kasashen waje jamiar Ahmadu Bello na Zaria.

A shekarar 2015 ya kammala digiri ta uku, ya zama dakta kan noma da ilimin kauye (doctorate in agriculture and rural sociology).

Aikin Dikko Radda

Aikin Dikko Radda
Aikin Dikko Radda

Umar Radda ya yi koyarwa a matsayin malamin makaranta daga shekarar 1989 zuwa 1999. Yayi aikin banki a tsohuwar banki FSB International bank daga shekarar 1999 zuwa 2003.

Aikin Siyasa Na Dikko Radda

Aikin Siyasa Na Dikko Radda
Aikin Siyasa Na Dikko Radda

Shekarar 2003, dikko yayi rikon kwaryar kujerar ciyaman na karamar hukumar Charanci, ya kuma zama ciyaman na karamar hukumar a shekarar 2005.

A shekarar 2013 ya kuma national welfare secretary na jam’iyar APC kamin ya zamo shugaban ma’aikatan gwamnan katsina, bayan Rt Hon Aminu Bello Masar iya zabe shi.

Dakta Dikko Radda ya zama zababben Darakta janar na Hukumar SMEDAN ranan 14 ga watan Maris shekarar 2016, wanda yayi aikin zango daya na shekara biyar.

Bayan aiki da yayi da gwamnati da masu zaman kansu wanda ya shafi tattalin arzikin kasa, ya kawo hanyoyi da dokoki wanda zasu bunkasa  kanana da madaidaita kasuwanci a kasar.

Ya ajiye aikin darakta janar na SMEDAN a watan Afrailu shekarar 2022 dan yayi takarar gwamna, yayin da suka shiga zaben firamare na jihar katsina. Dikko ya lashe zaben firamare na jam’iyar APC a jihar.

Kuma yaci zaben gwamna a zaben da ta gabata wanda akayi  ran 18 ga watan maris, hakan yazamo Gwamnan Jihar Katsina.

Karin Bayani Kan Dikko Radda

Karin Bayani Kan Dikko Radda
Karin Bayani Kan Dikko Radda

Radda ya kasance mai taimako sosai wanda hakan yakai da bude Gwagware Foundation a shekarar 2016 domin taimaka wa mutanen da basu da karfi da kuma horas da mutane kan sana’o’I domin su dogara da kansu. Sama da matasa 500 ya horas kan computer da dinkin kayan sawa.

Dikko yayi aure kuma yana da mata da yara.

Karramawan Dikko Radda

Karramawan Dikko Radda
Karramawan Dikko Radda

Dakta ya karamawa ta Award mai ta ke Distinguished Leadership Award daga Nigeria Civil Service Union a 2019.

Yasamu karramawa ta Public Sector Excellence Award a shekarar 2022 ta THE REVENUE magazine.

Hotunan Dikko Radda

 

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Watch African Stories

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button