
Zanyi Takarar Shugabancin Nijeriya – Osibanjo
Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo a safiyar ranar Litinin ya fito balo-balo ya ayyana burinsa na fitowa takarar kujerar shugaban kasar Nijeriya a zaben mai gabatowa 2023.
A cikin wani sakon bidiyo mai tsawon minti 6 da dakika 56 da Osibanjon ya wallafa a shafinsa na facebook, inda yake cewa, “A yau na fito na bayyana muradina na yin takarar kujerar shugaban Kasar Nijeriya a karkashin Jam’iyyar APC.”
Mutane dayawa nata rade-radin fitowar Mr Osibanjo tunda jimawa, a gefe guda kuma wasu ke ganin ba abu mai yiwuwa bane idan akayi laakari da Takarar uban gidanshi Ahmed Bola Tinubu.
Ko Ya Zata Kaya?
Discover more from Labaran Yau
Subscribe to get the latest posts sent to your email.