
Babbar tauraruwar Nollywood, Mercy Johnson ta isar da sakon ta ga jama’a a shafinta na sadar da zumunta; tace,
“Sa’ad da nake ‘yar shekara 16, a shekara ta 2000, na sami kaina ina aiki a matsayin mai aikin gida, ina yin duk abin da zan iya don tallafa wa iyalina.”
“Rayuwa ba ta da sauƙi, amma na ƙuduri niyyar ba da komai na, ƙauna da alhaki. Bayan shekaru hudu, a cikin shekarar 2004, ina shekara 20 wani abu mai ban mamaki ya faru.”

“Wani abokina da ya ga halina na rashin gajiyawa ya ba ni shawara, kuma ya tallatani ga mai shirya fim. Wannan lokacin guda ɗaya, ashe shi zai canza rayuwata har abada.
Na samu babban nasara harkar fim tare da taka rawa a cikin fim dina na farko wato “The Maid”.

Abin ban mamaki ne da gaske, don an bani yin kafcen aikin ’yar aikin gida kuma abu ne da nake yi a raywata kullum, kamar abu na biyune a gare ni domin ina yin wannan a rayuwa.”
“Kafce yakasance na keta raini, don ya kasance wani siffa na abubuwan da na gani a zahiri. Masu sauraro sun ji haka, haka ma masu suka. Ayyukana sun yi tasiri sosai har na sami lambar yabo ta Fitacciyar Jaruma a Najeriya.
Wancan fim din ba wani abu ne kawai ba; shine farkon tafiyata a matsayina na yar wasan kwaikwayo. Duk nasarar da kuka gani a yau shaida ce ga waɗannan gwagwarmayar farko.”

Ku fahimci cewa tafiyata tana da ƙalubale, juriya, da bangaskiya. Na gode wa Allah da ya ganni a wannan matakin, kuma yanzu na rungumi wannan sabon babi tare da godiya da farin ciki.” – Mercy Johnson