FootballLabaran YauTrending Updates

An Cika Ragar Kano Pillars Da Plateau United A Tsakiyan Gida – NPFL Ta Ɗau Zafii

A wasannin wannan sati na Nigerian Premier League, kungiyar Kano Pillers da Plateau United sunsha kashi a hannun Remo Stars da kuma Niger Tornadoes a tsakiyar gidansu, wanda suka cafki kwallaye bibbiyu a raga.

Gasar ta Nigerian Premier League (NPFL) ta fara cikin dachi ma wasu kungiyoyin da basu shirya mata ba da kyau ba, wasan tazo da nuna girma da sarautar iya taka leda.

Kungiyoyi masu karfi sun tsinci kansu a koma baya wurin yin shirin da ya kamata. Kungiyar Remo Stars sun fusata daga fara tafiya da daukan sarautar table din NPFL da point 9 a cikin wasanni 3 da kuma tara kwallaye ma abokan gasa.

Kungiyoyi masu taka rawar gani a da kamar su Plateau United sun kasance na 7 a table din da point 4 a cikin wasa 3.

Wasansu na uku da suka karbi bakoncin Niger Tornadoes, wanda suka kawo musu guzurin kwallaye biyu har dakin ragarsu. I. Okechukwu ne ya fara zura kwallo ta farko a minti 17 wanda ya bawa Tornedoes nasara a farko tashi.

Tun daga nan aka ta bugata kamar wuta inda Plateau United suka dage wuri daidaita kwallon amma babu nasara har aka cinye minti 90 aka kara mintuna, bayan anci minti 4 a karin, K. Ebong daga Niger Tornadoes ya kara narka wa ragar Plateau United wuta suka kara kwallo.

A minti 1 daya kuwa da cinsu ashe P. Samuel daga Plateau United ya fusata da kwallon karshe, hakan yasa ya bazama sai da ya narka kwallo daya a ragar Niger Tornadoes burin shi ya cika na hana su ‘clean sheet’

Niger Tornadoes suna na 3 a table da point 7 a wasa 3 yayinda suka biyo bayan Rivers United FC da suke na 2 a table suma da point 7 amma sun fi Niger zura kwallaye.

Kano Pillars sun buga wasa ta 3 wanda suka samu nasarar wasa 1 dayin kunnen doki 1 da kuma barar da 1. Hakan ya ajiyesu a na 6 a table din.

A ranar lahadi 22 ga watan September ne Remo Stars suka zo har gida suka zarge ragan Kano Pillars da kwallaye biyu da nema (2-0). Inda I. Sodiq ya zura kwallo na farko a minti 26 da fara wasa, sai F. Mawuena ya kara na biyu a minti 60.

Ba’a maganan su Kwara, Katsina, da Nasarawa United. Kwara United tana na 16 a table, Katsina United na 8 sannan Nasarawa United na 12 da point 2.

Karshen table din kuma ya kunshi su Lobi Stars, Bayelsa United, Ikorodu City, da Heartland Owerri su suke na, 17, 18, 19, da 20, a table din, wato ma’ana suke relegation.

Ga Sakamakon Wasannin Nigerian Premier League (NPFL) Da Aka Buga Yau September, 22nd 2024

1. Plateau United 1 Vs 2 Niger Tornadoes

17′ I. Okechukwu
94  K. Ebong

P. Samuel   95′

2. Heartland Owerri 0 Vs 0 Katsina United

3. Kano Pillars 0 Vs 2 Remo Stars

26′ I. Sodiq
60′ F. Mawuena

4. Sunshine Stars 0 Vs 0 Abia Warriors

5. Kwara United 0 Vs 0 Ikorodu City

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Watch African Stories

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button