KannywoodEntertainmentTrending Updates

Jerin Jarumai 14 Mafiya Arziki A Kannywood 2025

Jerin Jarumai 14 Mafiya Arziki A Kannywood 2025

Ga jerin manyan jaruman 14 mafiya arziki a cikin masana’antar Kannywood a wannan shekara ta 2025.

1. Ali Nuhu: Ana kiyasta cewa dukiyarsa ta kai kusan dala 1m (kimanin Naira miliyan 120).

2. Adam A. Zango: Dukiyarsa tana kusan dala 800,000.

3. Rahama Sadau: Tana da dukiya ta sama da dala 800,000.

4. Sani Musa Danja: Ana hasashen yana da dukiya ta dala 750,000.

5. Naziru Sarkin Waka: Mawakin kuma jarumin yana da kusan dala 500,000.

6. Yakubu Muhammad: Dukiyarsa tana kusan dala 500,000.

7. Nafisa Abdullahi: Tana da dukiya ta sama da dala $500 million

8. Sadiq Sani Sadiq: Ana kiyasta cewa yana da dala 500,000.

9. Garzali Miko: Dukiyarsa tana kusan dala 500,000.

10. Nuhu Abdullahi: Ana hasashen yana da dala 400,000.

11. Halima Atete: Tana da dukiya ta sama da dala $300,000.

12. Umar M. Shareef: Dukiyarsa tana kusan dala 165,000.

14. Lilin Baba: Ana kiyasta cewa yana da dala 33,000.

1. Ali Nuhu

Arzikin Ali Nuhu
Arzikin Ali Nuhu

Ali Nuhu yana da arzikin daya kai kusan dala miliyan ɗaya (kimanin Naira miliyan 120).

Wannan dukiya ta samo asali ne daga aikinsa a fina-finai sama da 500 na Kannywood da Nollywood, tallace-tallace, da kuma harkokin kasuwanci.

Shine Manajan Daraktan Hukumar Shirya Fina-Finai ta Najeriya (Nigerian Film Corporation).

Ali Nuhu ya kasance jakadan kamfanoni da dama, ciki har da Colgate-Palmolive, Mouka, , Sumal Foods Limited, Globacom, OMO, Samsung, da Checkers Custard.

A shekarar 2018, ya sami digirin girmamawa daga Jami’ar ISM Adonai American University da ke Jamhuriyar Benin.

  • Ali Nuhu yanada masoya samada million 3 a Instagram: @realalinuhu
  • Ali Nuhu yanada masoya samada million 3.6 a Facebook: Ali Nuhu Mohammed
  • Ali Nuhu yanada masoya da yawa a X (wato Twitter): @alinuhu
  • Ali Nuhu yanada masoya da yawa a YouTube: Ali Nuhu

2. Adam A. Zango

Arzikin Adam A. Zango
Arzikin Adam A. Zango

Adam A. Zango yana da arzikin daya kai kusan dala 800,000. Wannan adadi ya samo asali ne daga aikinsa a matsayin ɗan fim, mawaki, darekta, kuma marubucin fina-finai a masana’antar Kannywood.

Adam A. Zango ya fara sana’arsa ne a shekarar 2001 a matsayin mai tsara waƙoƙin fina-finai, sannan ya zama ɗan fim, inda ya fito a sama da fina-finai 100.

Adam A. Zango ya kasance jakadan kamfanoni da dama, ciki har da MTN Nigeria, INEC, da kuma PDP

Bugu da ƙari, yana da tashar YouTube mai suna “Adam A. Zango Official” wadda ke da masu biyan kuɗi sama da 908,000, kuma an kiyasta cewa tana samar masa da kusan dala 1,890 a kowane wata.

A shekarar 2019, ya bayar da tallafin Naira miliyan 47 don taimakon yara marasa galihu su ci gaba da karatunsu

  • Instagram: @adam_a_zango yana da mabiya miliyan 2.
  • TikTok: @iam_adam_a_zango yana da mabiya miliyan 2 da kuma likes miliyan 20.
  • Facebook: Shafinsa na Facebook yana da mabiya miliyan 1.
  • X (wato Twitter): @princeazango yana da mabiya 226,100.

3. Rahama Sadau

Arzikin Rahama Sadau
Arzikin Rahama Sadau

Rahama Sadau: Tana da Arziki ta sama da dala 800,000. Rahama Sadau fitacciya kuma babbar jaruma ce, mai shirya fina-finai, a masana’antar Kannywood da Nollywood.

An haife Rahama Sadau a ranar 7 ga Disamba, 1993, a Kaduna, Najeriya. Ta fara fitowa a fina-finai a shekarar 2013, ta samu lambobin yabo da dama, kamar su “Best Actress (Kannywood)” a City People Entertainment Awards a shekarar 2014 da 2015.

  • A Instagram: tana da followers fiye da miliyan 3.4
  • A Facebook: tana da followers fiye da 1.5

Idan Kana Bukatan: Rayuwa da Tarihin Jaruman Kannywood

4. Sani Musa Danja

Arzikin Sani Musa Danja
Arzikin Sani Musa Danja

Sani Musa Danja: Ana hasashen yana da Arziki ta dala 750,000. Sani Musa Danja, wanda aka haifa ranar 20 ga Afrilu, 1973, a garin Fagge, Kano, Najeriya,

Sani Musa Danja  ya kasance ɗaya daga cikin fitattun jarumai, masu shirya fina-finai, daraktoci, mawaka, kuma masu rawa a masana’antar Kannywood da Nollywood.

  • A Instagram: yana da followers fiye da miliyan 1.
  • A Facebook: yana da followers fiye da 80,000.

5. Naziru Sarkin Waka

Arzikin Naziru Sarkin Waka
Arzikin Naziru Sarkin Waka

Naziru Sarkin Waka: Mawakin kuma jarumin yana da Arzikin kusan dala 500,000. Naziru M. Ahmad, wanda aka fi sani da Naziru Sarkin Waka, ficaccen mawakin Hausa ne a Najeriya.

An haife Naziru Sarkin Waka a ranar 4 ga Satumba, 1986, a jihar Kano, Najeriya.

A shekarar 2018, Sarkin Kano ya naɗa Naziru Sarkin Waka a matsayin Sarkin Wakan Sarkin Kano, wato babban mawakin fadar Sarkin Kano.

Naziru ya fitar da waƙoƙi sama da 300 a cikin aikinsa, ciki har da “Sai Mun Bata Wuta Atiku Abubakar” da aka saki a shekarar 2022.

Haka zalika, yana da mabiya sama da 11,700 a shafin Spotify.

  • A Instagram: yana da followers fiye da miliyan 2.
  • A Facebook: yana da followers fiye da 66.1.

6. Yakubu Muhammad

Arzikin Yakubu Mohammed
Arzikin Yakubu Mohammed

Yakubu Mohamead: Dukiyarsa ta Arzikin kusan dala 500,000. Yakubu Mohammed, an haife shine ranar 25 ga Maris, 1973, a jihar Gombe, Najeriya.

Yakubu Mohammed ya kasance ɗaya daga cikin fitattun jarumai, masu shirya fina-finai, daraktoci, mawaka, kuma marubuta a masana’antar Kannywood da Nollywood.

Ya fara fim ne a shekarar 1998, yana rubuta labarai da aiki a bayan fage kafin ya fara fitowa a fina-finai.

Tun daga lokacin, ya fito a fina-finai sama da 100 na Hausa da kuma fiye da 40 na Turanci, ciki har da “Sons of the Caliphate,” “Lionheart,” “MTV Shuga,” da “4th Republic.”

  • A Instagram: yana da followers fiye da miliyan 1.
  • A Facebook: yana da followers fiye da 80,000.

7. Nafisa Abdullahi

Arzikin Nafisa Abdullahi
Arzikin Nafisa Abdullahi

Nafisa Abdullahi: Tana da arzikin ta sama da dala $5 million. Nafisa Abdullahi fitacciyar jaruma ce a masana’antar Kannywood, kuma tana da kasuwanci da dama. A watan Agustan 2022, ta kaddamar da kamfanin yin jakunkunan mata mai suna NAAF Luxury.

Haka zalika, tana da mabiya sama da 436,000 a shafin TikTok.

  • A Instagram: tana da followers fiye da miliyan 2.3
  • A Facebook: tana da followers fiye da 2.1

8. Hadiza Aliyu Gabon

Arzikin Hadiza Aliyu Gabon
Arzikin Hadiza Aliyu Gabon

Hadiza Gabon: Tana da arzikin ta sama da dala $300,000. Hadiza Gabon shahararriyar jaruma ce tana kuma mai shirya fina-finai a masana’antar Kannywood, ta yi fice a fina-finai da dama tun fara fim dinta a shekarar 2009.

Hadiza Gabon, tana da kamfanin dake taimakon jama’a mai suna HAG Foundation, wanda yake tallafawa al’umma ta hanyoyi da dama.

  • A Instagram: tana da followers fiye da miliyan 2.9
  • A Facebook: tana da followers fiye da 1.7

9. Sadiq Sani Sadiq

Arzikin Sadiq Sani Sadiq
Arzikin Sadiq Sani Sadiq

Sadiq Sani Sadiq: Yana da arzikin sama da dala 500,000. Sadiq Sani Sadiq ya taka rawar gani a masana’antar Kannywood tun fara warsa a shekarar 2004. Ya fito a fina-finai sama da 200.

kuma, ya samu lambobin yabo da dama, ciki har da Best Actor a gasar Kannywood Awards ta shekarar 2015.

  • A Instagram: yana da followers fiye da miliyan 1.6
  • A Facebook: yana da followers fiye da 80,000.

10. Garzali Miko

Arzikin Garzali Miko
Arzikin Garzali Miko

Garzali Miko: arzikin sa ta kusan dala 500,000. Garzali Miko babban mawaki ne kuma fitaccen jarumi a masana’antar Kannywood, wanda ya yi suna a waka da fina-finai. Ana iya samun sabbin wakokinsa da bidiyoyi a tashar YouTube dinsa.

  • A Instagram: yana da followers fiye da 899.4
  • A Facebook: yana da followers fiye da 80,000.

11. Nuhu Abdullahi

Arzikin Nuhu Abdullahi
Arzikin Nuhu Abdullahi

Nuhu Abdullahi Yana arzikin daya kai kusan dala 400,000. Nuhu Abdullahi yana ɗaya daga cikin fitattun jaruman Kannywood.

Nuhu Abdullahi ya fara fim ne a shekarar 2009 a matsayin mai shirya fina-finai. Ya yi suna a fina-finai da dama kamar “Kanin Miji”, “Baya da Kura”, da “Ana Wata ga Wata”, da kuma “Labarina”.

  • A Instagram: yana da followers fiye da 1.1
  • A Facebook: yana da followers fiye da 155,000.

12. Umar M. Shareef

Arzikin Umar M. Shareef
Arzikin Umar M. Shareef

Umar M. Shareef: Arzikin ta kusan dala 165,000. Umar M. Shareef shahararren mawaki ne kuma babban jarumi a masana’antar Kannywood, wanda ya yi sune a fagen waka da fina-finai. Ana iya samun sabbin wakokinsa da bidiyoyi a tashar YouTube dinsa.

  • A Instagram: yana da followers fiye da miliyan 1.7
  • A Facebook: yana da followers fiye da 1.4

13. Lilin Baba

Arzikin Lilin Baba
Arzikin Lilin Baba

Lilin Baba: Yana da arzikin sama da dala 33,000. Lilin Baba, wanda aka haifa ranar 1 ga Janairu, 1992, a Gwoza, Jihar Borno, Najeriya

Lilin Baba babban mawaki ne, marubuci, ɗan fim, kuma ɗan kasuwa a masana’antar Kannywood.

A shekarar 2019 ya yi suna a fim ɗinsa na farko mai suna “Hauwa Kulu”. ya kuma lashe kyautar “Arewa Best RnB Music Act of the Year” a gasar City People Entertainment Awards. A ranar 18 ga Yuni, 2022.

  • A Instagram: yana da followers fiye da 677.4
  • A Facebook: yana da followers fiye da 80,000.

14. Halima Yusuf Atete

Arziki Halima Yusuf Atete
Arziki Halima Yusuf Atete

Halima Atete: Tana da arziki ta sama da dala $300,000. Halima Atete babbar jaruma ce kuma tana shirya fina-finai a masana’antar Kannywood. An haifeta ne a ranar 26 ga Nuwamba, 1988, a garin Maiduguri, dake Jihar Borno, Najeriya.

Ta shiga harkar fim ne a shekarar 2012 wan da fim ɗinta na farko shine mai suna “Asalina”. Daga baya, ta fito a fina-finai sama da 160.

A shekarar 2013, ta samu damar lashe kyautar “Best New Actress” a City People Entertainment Awards.

  • A Instagram: tana da followers fiye da miliyan 1.4
  • A Facebook: tana da followers fiye da 80,000.

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Watch African Stories

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button