Biography

Cikakken Tarihin Muhammad Adamu Aliero, Rayuwarsa, Karatunsa, Siyasarsa, Iyalensa, Aikinsa, Hoyunansa

Cikakken Tarihin Muhammad Adamu Aliero 

Labaranyau.com ta kawo muku tarihi da cikakken bayani kan rayuwa, karatu, siyasa da sauransu kan Sanata Adamu Aliero.

Chikekken Tarihin Muhammad Adamu Aliero 
Cikakken Tarihin Muhammad Adamu Aliero

Asalin Adamu Aliero

Adamu Aliero Dan jihar kebbi ne wanda aka haifeshi ranar 1 fa watan junairu shekarar 1957. Dan siyasa ne a kasan najeriya . Ya riqe muqamin sanata na mazabar jihar kebbi ta tsakiya daga shekarar 2007 zuwa 2008. Ya kuma riqe sanata daga 2015 zuwa 2019, kuma yayi Gwamna a jihar daga 1999 zuwa 2007. Tsohon Dan jam’iyar PDP ne.

Tsohon Shugaban kasar Najeriya Umaru Musa Yar’Adua ya zabe shi a matsayin Ministan Birnin tarayya a shekarar 2008. Ya bar ofishin minista a shekarar 2010 bayan Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya dakatar da ministoci.

DOWNLOAD MP3

Rayuwa Da Karatun Adamu Aliero

Rayuwa Da Karatun Adamu Aliero
Rayuwa Da Karatun Adamu Aliero

Adamu haifaffen Aliero, karamar hukumar Aliero da ke jihar kebbi. Ya samu karatun a makarantar addinin musulunci, ya fara karatun Firamare a shekarar 1965 a makarantar Aliero Town Planning.  Sannan ya wuce gaba yayi karatun sakandare a makarantar sakandare na gwamnati na Koko in da ya kammala a shekarar 1976.

Bayan nan ya wuce School of Basic Studies ta jami’ar Ahmadu Bello inda yayi IJMB ya kuma karanta fasahar siyasa nan ya gama digiri a shekarar 1980.

Aikin Adamu Aliero

Aikin Adamu Aliero 
Aikin Adamu Aliero

A shekarar 1981 ya fara aiki a matsayin administrative Officer a kwalajin Ilimi ta sokoto, sannan ya shiga aikin imagireshan a wannan shekarar. A shekarar 1997 ya bar aikin sa inda ya shiga harkan kasuwanci da shiga da fitar kaya.

DOWNLOAD ZIP

Siyasar Adamu Aliero

Siyasar Adamu Aliero 
Siyasar Adamu Aliero

Ya shiga harkar siyasa a shekarar 1998 a tsohuwar jam’iyar UNCP (United Nigeria Congress Party), yayi takara yaci zaben Sanata don wakiltar mazabar jihar kebbi ta tsakiya, inda aka soke zaben bayan mutuwar Shugaban kasa Sani Abacha. Bayan samun sabuwar gwamnati, A shekarar 1999 Aliero ya yi takarar Gwamna kuma lashe zaben a jam’iyar APP, an rantsar dashi ran 29 fa watan mayu 1999.

Aliero ya Kara takara ya kuma lashe zabe a shekarar 2003. Yana daga cikin gwamnoni tsiraru da suka koma kujerar su bayan gwamnatin kasa mai ci Ta samu a jam’iyar PDP. Jam’iyar APP ta samu canji zuwa ANPP a shekarar 2003.

Aliero ya bar ANPP ya koma PDP a shekarar 2007, inda yayi takarar sanata ya kuma lashe zaben. Shi sanata ne na kebbi ta tsakiya.

Yayi canje canjen jam’iya ya koma PDP bayan yin shekara a jam’iyar CPC a 2012. Sai ya Kara komawa jam’iyar APC inda ya bar PDP a shekarar 2014. Shi da mukarrabansa tun shekarar 1999 kamar tsohon Shugaban jam’iyar CPC ta jiha Sani Jauro duka suka koma APC.

Ya samu muqamin ciyaman na kwamitin duba ga lamuran Land transport  na Majalisan dattawa na Goma ranar 8 ga augusta 2023.

Iyalen Adamu Aliero

Iyalen Adamu Aliero
Iyalen Adamu Aliero

Adamu Aliero yana da mata uku, sun hada da Maimuna, zainab da Aaliyah. Ya haifi yara 11, maza 10 mace 1. Sun hada da Sadiq, Mustapha, Abdulazziz, Aliyu, Umar, Ayman, Adamu, Khalil, Abubakar da Fatima. Duka mazauna Abuja.

Hotunan Adamu Aliero

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Check Also
Close
Back to top button