Cikekken Tarihin Atiku Bagudu
Yau shafin mu ta labaranyau.com ta kawo muku cikakken tarihi da bayani kan rayuwa, karatu, Siyasasa da kuma Iyalen Sanata Atiku Bagudu.
Rayuwar Atiku Bagudu
Atiku Bagudu CON, Dan siyasa ne a najeriya wanda shine a yau shekarar 2023 yake matsayin Ministan kasafin kudi da tsare tsaren kasa. Yayi gwamnan jihar Kebbi daga shekarar 2015 zuwa shekarar 2023. Ya kuma riqe muqamin sanata na mazabar Kebbi ta tsakiya daga shekarar 2009 zuwa 2015.
An haifi Atiku Bagudu ranar 26 ga watan disamba na shekarar 1961. Atiku ya fito daga gidan kudi, Mahaifinshi ya riqe muqamin Darakta na Ilimin firamare na jihar Kebbi. Bagudu ya tashi cikin gata da kuma yelwan rayuwa. Ya auri zainab bagudu.
Karatun Atiku Bagudu
Atiku Bagudu yayi makarantar firamare da sakandare a jihar Kebbi, Yayi digirin sa na farko a jami’ar Uthman Danfodiye Na jihar sokoto inda ya gama da digiri kan tattalin Arziki (Economics). Ya koma jami’ar Jos na jihar Filato inda yayi digirinsa na biyu MSc Economics. Kuma ya karayin wata digiri ta biyu kan M.A International Affairs.
Siyasar Atiku Bagudu
A shekarar 2009 Bagudu ya zama sanata, inda ya maida gurbin Adamu Aliero yayin da lashe zaben By-Election da akayi bayan Tsohon shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan Ya baiwa Aliero Muqamin Ministan Birnin Tarayya a watan disamba na shekarar 2008. Ran 6 ga watan Afrailu na shekarar 2011 anyi zaben da bagudu ya lashe zaben a jam’iyar PDP da kuri’u 173,596 bayan Aliero ya koma CPC ya zo na biyu da kuri’u 137,229. Aliyu Bello Muhammad yazo na uku da kuri’u 11,953 a jam’iyar ACN.
A lokacin zaben 2015 Bagudu ya koma jam’iyar APC ya bar PDP inda yayi takarar gwamna a jam’iyar APC kuma yaci.
A zaben shekarar 2019 Bagudu ya lashe zaben gwamna da kuri’u 673,717 yayin da ya doke Sanata Isa Galaudu na jam’iyar PDP wanda yazo na biyu da kuri’u 106,633.
Bagudu ya sake takarar Gwamna a jihar kebbi a shekarar 2023 inda Aliero na PDP ya lashe zaben bayan yabar jam’iyar APC saboda ya fadi zaben Firamare.
Atiku ya zama Ministan kasafin kudi da tsare tsare na kasa yayin da Shugaban kasa tinubu ya zabe shi domin wannan aiki ranan 16 fa watan Augusta 2023.
Karamawar Atiku Bagudu
A watan Oktoba 2022, bagudu ya samu Karramawa ta kasa CON (Commander of the order of Niger) wanda Tsohon shugaban kasa Buhari ya bashi.
Iyalen Atiku Bagudu
Bagudu yana da yara wanda sun hada da Maryam Bagudu, Ibrahim Bagudu, Bello Bagudu, Aisha Bagudu da sauransu
Hotunan Atiku Bagudu