FootballLabaran HausaTrending Updates

Amsoshin Ruben Amorim Bisa Kuskurenshi Na Kyautar Da Wasan Tottenham A Banza

Amorim Ya Maida Martani Wa Duniya Bisa Kuskurenshi A Hiran Bayan Wasa Na Kyautar Da Wasan Tottenham Na Ranar 16 Ga Watan Febureru 2025 Wanda Manchester United Tasha Duka (1 - 0)

Ruben Amorim ya sha kalubalanci daga sassa daban daban bisa ga taurin kai da rashin lissafin da ya nuna yayin da Manchester United ke shan kashi a hannun Tottenham da ci 1-0 a ranar 16 ga Fabrairu, 2025.

Hakan ya jawo maida martani in da ya fara da bayyana rashin jin dadinsa da matsalar rauni (injury) da kungiyar ta tsinci kanta.

Ya nuna cewa kulob din ya rasa ’yan wasa 12 na farko, wanda hakan ya tilasta masa sanya wasu matasa takwas da ba a gwada su ba a kan benci tare da tsohon soja Victor Lindelöf.

Kuma yayi magana game da rashin Christian Eriksen, wanda bai buga wasan ba saboda matsalolin lafiya da ke da alaka da yanayin zuciyarsa.

Ya ce dole ne  kulob din ya yi taka-tsan-tsan game da lafiyar Eriksen, yana mai bayyana bukatar yin taka-tsan-tsan wajen kula da yanayinsa.

Amorim ya nuna tirjiyanshi na jaddada mahimmancin mai da hankali kan cin nasara a wasanni masu zuwa maimakon yin la’akari da yanayi mai faɗi.

Tottenham 1 - 0 Manchester United - 16th February, 2025
Tottenham 1 – 0 Manchester United – 16th February, 2025

Amsoshin Kocin Manchester United, Ruben Amorim Akan Wasan Tottenham

Kalmomin Ruben Amorim Na Taron Bayan wasa:

1. Akan Daman Maki

Amorim yafara da banbancin na daman makkin wasan, ya nuna cewa yana sane da damanmakin da akayi wasa dasu, inda yace;

“Babban bambanci a wasan shi ne, su [Tottenham] sun zira kwallo mu kuma mun kasa. Mun sami damar zira kwallaye dayawa amma a banza, sannan munfi matsa su a farkon rabin lokaci.”

“Mun sha wahala a wurin canje-canje na kokarin samun sakamako, amma dukda haka a karshe su zira kwallaye kuma ya gagara.”

“Muna buƙatar sanya kwallon a cikin raga saboda mun sami wasu daman, mun kirkiro wasu daman makin da za mu iya haifar da nasara, wanda a cikin wasan shine mafi wuya.”

“A yau mun samar da damammaki amma muna bukatar mu zura kwallo a raga don samun nasara a wasanni.”

2. Akan Raunin (injury) ‘Yan Wasa

Yace;

“Sai kun fara da wata tsari. Sannan kuta bukatar ganin mako mai tsawo na dogon lokaci. Kuma kun yi aiki da ka’idodinku yanda yakamata amma kowace rana, sai ku rasa ‘yan wasan da sukesa canza tsarin ku na wasan.

“Ba zan iya yin wasa da Joshua [Zirkzee] ba kamar yadda zanyi da Amad.”

Joshua Zirkzee, Ruben Amorim, and Amad Diallo
Joshua Zirkzee, Ruben Amorim, and Amad Diallo

“Sannan a lokacin da nake son Bruno [Fernandes] ya isa kan kwallon dan tsarin gina neman sakamako saboda yana da kyau sosai wurin canza wasa.”

“Amma kuma ya kasance shine zai dinga saka tsanani gurin kwatan kwallon ai abune me wuya sosai. Yana da kuma wuyar gaske lokacin da kake buqatar ‘yan wasan su mayar da martani kuma kayi ta canje-canje a tushe.”

Bruno Fernandez (Tottenham 1 - 0 Manchester united)
Bruno Fernandez (Tottenham 1 – 0 Manchester united)

“Tsarin 4-4-2 a low block yana da wuya buga wasa da wannan tawagar fiye da abin da muka yi a yau. A ra’ayina na suna da budewa da kuma shimfiɗa a tsarin wasan ƙungiyar.”

“Abin da kuke gani da abin da kuke tattaunawa a kowane mako ina gani kuma ina sane. Ina da matsaloli da yawa, aikina yana da wuyar gaske a nan. Amma na tsaya tare da imani na.”

3. Akan Dawowan ‘Yan Wasa Daga Rauni

Yace;

“Rauni da yanayin rashin lafiya a wannan makon ba kome ba ne in ya kasance a baya ne. Muna brin mu dawo da ‘yan wasan, ina ganin wasu za su iya dawowa a wasa na gaba [da Everton].

“Daga wannan lokacin har zuwa karshen kakar wasa, haka zai kasance don haka dole ne mu kasance tare don kammala kakar wasa sannan kuma mu fara wata.”

4. Akan Rashin Bayar Ma Yara Dama

Amorim yace;

“Wannan ita ce gasa mafi wahala [Premier League] a duniya. Ina ƙoƙarin yi ahankali da su. Naki yin canji saboda naga kungiyar tanakokarin matsawa sai na ji babu bukatan canji.

“Amma za su yi wasa, dole ne su kasance cikin shiri. Suna ƙoƙarin karanta wasan, suna ƙoƙarin fahimtar abin da suke gani a horo.”

5. Akan Kokarin ‘Yan Wasan

Amorim yace;

“Ina ganin abu mafi kyau shi ne a manta da abin da ya gabata. Kada ku mai da hankali kan jadawalin, kada amai da hankali kan wannan lokacin, kada ku mai da hankali kan yanxu.

“Aiki ne kawai zalla ya rage a wannan mako, sai kuma shiryawan wasan. Sai wasa na gaba kuma za mu yi kokarin samun nasara a wasan.”

Sakon Kocin Manchester United Zuwa Ga (Fans) Magoya Baya
Sakon Kocin Manchester United Zuwa Ga (Fans) Magoya Baya

Sakon Kocin Manchester United Zuwa Ga (Fans) Magoya Baya

Ruben Amorim bayan maida martani ga dukkan korafe korafe da ake tayi ya mika sakon sa suwaga magoya baya kamar haka;

“Tallafin goyon bayansu yana da matukar mahimmanci. Kamar yadda na fada a cikin wannan makon, wani lokacin yana da matukar wahala a fuskance su a wannan lokacin amma muna yin komai, nima ina yin komai.”

“Wani lokaci za mu iya yin nasara ko a’a; a cikin wannan halin, muna son su san cewa mun san suna son ganin ƙarin ƙoƙarii.”

“Kuma muna ƙoƙarin duk abin da zai juya abubuwa. Za mu yi wannan makon kuma a wasa na gaba, muke so.”

“Ban damu ba indan ta kainane. Na fahimci magoya bayanmu, abin da mutane da kafofin watsa labaru ke tunani game da shi.

A yanzu burina shine ina so in gama gasar da karfi, ban damu da ni ba, na damu da kulob din, da tawagar, da ‘yan wasa. Na tsani yin rashin nasara; yana matukar ratsa ni. Sauran damuwan ba na tunani game da.

“Ina so in taimaka wa ‘yan wasa na. Na fahimci halin da nake ciki, aiki na, ina da kwarin gwiwa game da wasanni na kuma ina so in ci gaba da wasanni, damuwata ba kai na bane.”

  • Tottenham 1 – 0 Manchester United Match Highlights: 

Labarai Masu Alaka:

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Watch African Stories

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button