Labaran Yau

[HOTUNA] Tinubu Yadawo Daga Taron AU Da Ya Halarta A Kasar…

Tinubu Yadawo Daga Taron AU Da Ya Halarta A Kasar Kenya

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya sauka Abuja bayan ya samu nasarar halartar taron koli na tsakiyar shekara na AU karo na 5 wanda aka gudanar a kasar Kenya.

Shugaban kasar ya sauka a jirgin s ana Air Force 001 a Abuja da misalign karfe 3 na ranar yau Lahadi 17 ga watan Yuli shekarar 2023.

Wadanda suka tari shugaban na Najeriya a lokacin da ya sauka a airport din sun hadar da Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, COS ne ya karbe shi, Shugaban maaikatan shugaban kasar Femi Gbajabiamilia shima yana nan, tare da wasu manyan maaikatan nasa.

Akwai Gwamnan Jihar Imo Sanata Hope Uzodimma da Tsohon Gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje.

Ga Hotuna daga bisani ⇓

 

Shugaba Tinubu Yayi Jawabi A Taron AU A Kasar Kenya

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu yayi jawabin nasa ne a yau ranar Lahadi a wajen taron hadin gwiwa karo na biyar na tsakiyar shekara (5thMYCM) na kungiyar Tarayyar Afirka (AU), da kungiyoyin tattalin arziki na yankin (RECs), hanyoyin yankin (RMs), da kuma kasashe mambobin kungiyar AU.

Tinubu ya amince da kalubalen da Afirka ke fuskanta da suka hada da ta’addanci da kuma sauya gwamnati da ba ta dace ba. Ya kara da cewa cikar hadakar da ake nema ba zai yuwu ba matukar kasashe da dama sun tsaya cikin tashin hankali da yaki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button