
Tuwon Amala ta samo asali ne daga kabilar yarbawa (Yoruba), ita ce tuwon da akafi cinsa a kasar yarbawa.
Duk da dai a yau mutane daga kabilu daban daban sun koyi ci Kuma suna ci sosai ko lokacin da ta kama.
Abubuwan Hada Tuwon Amala
1. Garin bawon doya kofi biyu
2. Garin alabo( garin rogo) kofi 1
3. Ruwa
4. Tukunya
5. Muciya
Yadda Ake Hadawa
- Tankade kofi daya na garin bawon doyan daban a wani kwano.
- Dauko garin alabon kofi daya da garin bawon doyan kofi daya sai a hada su gu daya a tankade a wani kwano daban.
- Daura tukunya akan wuta, sa ruwa daidai yanda tuwon ba zai yi ruwa ruwa ba kuma bawai ya yi tauri ba rufe tukunya nadan wani lokaci.
- Sai a dauko garin bawon doyan wanda aka tankade kofi daya da farko asa masa ruwa a dama.
- Idan ruwan ya tafasa sai ayi rude a rufe nadan wani lokaci.
- Dauko garin alabon wanda aka hadashi da garin bawon doyan a tuka sai a rufe tukunyan na dan wani lokaci kadan.
- Sai a sauke a sake tukawa ki kwashe a kula ko ki daure su a leda.

Ana cinshi da kowani irin miya.