Biography

Cikakken Tarihin Usman Ododo, Rayuwarsa, Siyasarsa, Karatunsa, Aikinsa, Iyalansa, Arzikinsa, Hotunansa

Cikakken Tarihin Usman Ododo

Ahmed Usman Ododo cikakken Dan siyasa ne wanda ya shahara a najeriya kuma aka san shi da tsari da shugabanci. Ya taso ne cikin masu ilimi hakan ya taimaka masa wajen so ya taimaka wa mutane har da kasa baki daya.

Cikakken Tarihin Usman Ododo 
Cikakken Tarihin Usman Ododo

Usman ya lashe zaben gwamna da akayi na nowamba shekarar 2023 a jihar Kogi. Ya kasance Dan siyasa ne wanda ke jam’iyyar APC.  Dan Ilimi da yake dashi kan Political science da Public Administration, ya riqe muqamin Odita janar na jiha na kananan hukumomin gwamnati.

An san Usman Ododo da kyauta da dattako, da kuma kula da iyali.

Rayuwar Usman Ododo

Rayuwar Usman Ododo 
Rayuwar Usman Ododo

An haifi Usman Ododo ran 7 ga watan fabrailu shekarar 1982, a jihar kogin najeriya. Shi asalin sa nan qabilar Ebira ne, qabilar Ebira ta sharaha a jihar kogi.

Ododo yayi aure yana da mata mai suna Aisha Ododo.  Yana da yara uku biyu maza da mace daya. Ya kasance yana jin dadin zama uba da kuma miji wa yaransa da matar sa. Yana tafiyantar da rayuwarsa ne bisa koyaswa na addinin musulunci.

Ya tashi cikin rufin asiri, hakan ya bashi damar fita dan aiki wa mutane da kuma kasa baki daya. Maihaifiyar sa Hajiya Fatima Ododo sananiyar Mai bada ilimi ne da yawan taimako. Mahaifinshi kuma Alhaji Ahmed Ododo sananne a kan harkansa na kasuwanci da kuma jagoranci cikin harkokin yau da kullum.

Karatun Usman Ododo

Karatun Usman Ododo 
Karatun Usman Ododo

Usman ya taso cikin rufin asiri, kuma ya samu karatu na Hakika a karamin shekaru. Yayi karatun sakandaren sa a federal government college Okene, A inda ya riqe matsayin Head Boy a makarantar.

Ya shiga an gwabza dashi a harkar kwallon kafa, wasan kwaikwayo, debate da Sauransu.

Ya cigaba da karatun sa ne a Jami’ar Ahmadu Bello wadda ta ke zaria. A nan ya samu digirin sa na farko akan fasahar siyasa (Political science) a shekarar 2004.  Ya kuma samu digiri ta biyu a fannin public administration a wannan jami’ar zaria a shekarar 2008.  A yanzu haka yana digirin digirgir wato digiri ta uku kan Political science a jami’ar Abuja da ke gwagwalada.

Aikin Usman Ahmed Ododo

Aikin Usman Ahmed Ododo 
Aikin Usman Ahmed Ododo

Mafi yawan aiki da yayi, yayi ne a fannin da ya karanta. Ya riqe mukamai na siyasa daban daban da kuma wasu irin ciyaman na matasan jihar kogi, Special Assistant wa Gwamna da kuma mamba na majalisan dokokin matasan kasa.

Ta wannan mukamai da ya rike, ya samu din bim basira da gogewa kan harkan aiki. Da kuma fahimtar matsaloli da ke fuskantar jihar shi da kasa baki daya. Ya kai da babu abunda yake gaban shi sai dai ya hado Kawunan mutane waje daya dan yin abinda ya dace dan cigaban al’umma.

Yana daga cikin yan siyasa masu tashe,  Ododo ya samu shahara bayan zabarsa da Yahaya Bello yayi a matsayin Audita Janar na Kananan hukumomi a jihar a shekarar 2019.

Yayi aiki har zuwa shekarar 2023 kuma ya kula da kudin jama’a na fannin kananan hukumomi. Ajiye aikin da yayi a shekarar 2023 ta bayyana niyyar sa na neman takarar gwamnan jihar kogi.

A watan wamba na shekarar 2023, ya lashe zaben gwamna a jam’iyar APC. Hukumar zabe ta bayyana shi a matsayin wanda yaci zaben da ta gabata. Wanda ya doke Dino Melaye na PDP da Alake na SDP.

Arzikin Usman Ahmed Ododo

Arzikin Usman Ahmed Ododo 
Arzikin Usman Ahmed Ododo

Ododo ya samu arziki kan harkar siyasa da kasuwanci daban daban. Ya zuba hannun jari a kampani daban a fadin kasar tun daga noma, gine gine wanda ya bashi arzikin kaddarori a gida najeriya da kasashen waje.  Yana shiga motoci na alfarma kuma yana rayuwa ne cikin Jin dadi.

Yana rayuwa ne a kaskance kuma baya albazzaranci. Yana amfani da arzikin shi wajen taimako, sadaka da kyau. Ana kiyasin yana da arziki na kimanin dala miliyan Goma.

Hotunan Usman Ahmed Ododo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button