Biography

Cikakken Tarihin Aminu Alan Waka, Rayuwarsa, Karatunsa, Aikinsa, Wallafawarsa, Wakarsa, Iyalansa, Karramawansa, Hotunansa

Cikakken Tarihin Aminu Alan Waka 

Shafin labaranyau.com ta kawo muku cikakken tarihi da bayani kan Aminu Alan waka bisa gwargwarmaya, fikira da kuma shaharan sa ta fagen waka da rubutu.

Cikakken Tarihin Aminu Alan Waka 
Cikakken Tarihin Aminu Alan Waka

Rayuwar Aminu Alan Waka

Asalin sunan sa Aminu Ladan Abubakar wanda aka fi sani da Alan Waka, An haifeshi ranar 11 ga watan fabrailu na shekarar 1973 a jihar kano na kasar najeriya. Dan asalin jihar kano ne kuma ya samu karatu da shahara a kanon dabo.

Allah ya albarkace shi da fikira ta rubutu da waka wanda akansu ya samu sanuwa a idon duniya da kuma samun girma ko sarauta na sarkin mawakan hausawan duk duniya.

Karatun Aminu Alan Waka

Karatun Aminu Alan Waka 
Karatun Aminu Alan Waka

Aminu Ala yayi karatun firamare dinsa a firamaren Tudun Murtala a tsakanin shekarar 1980 zuwa 1986, sai ya wuce gaba dan karatun sakandare a GSS Kawaji a Dakata tsakanin shekarar 1987 zuwa 1992. Ya kuma shiga jami’a don karin karatu a shekarar 2004 inda ya samu takardan diploma a shekarar 2007 a  school of technology duka a jihar Kano.

Wallafan Aminu Alan Waka

Wallafan Aminu Alan Waka 
Wallafan Aminu Alan Waka

An fara sanin Aminu Ala a fannin rubutun Hausa kamin ya samu sanuwa a fannin waka. Ala ya wallafa litattafai guda tara daga ciki akwai su:

  • Cin Zarafi
  • Cin fuska
  • Bakar Aniya
  • Sawaba
  • Jirwaye
  • Tarzoma

Wakar Aminu Alan Waka

Wakar Aminu Alan Waka 
Wakar Aminu Alan Waka

Ala ya fara waka tun Yana dalibin makarantar islamiyya inda ake koyas dasu karatun addini ta hanyar wake, Saboda suyi saurin dauka da fahimta. Anan aka koyar dasu wakokin yabon manzon Allah lokacin maulidi.

Saboda wa samun horaswa ta fannin wakar yabon manzo, Ala Yana daga cikin wanda suka riqi koyaswan kuma suka ci nasara a fannin wake da wakokin Manzo.

Bayan ya girma sai ya cigaba da rubutawa Yana rairarawa.

Ala Yana da Album na wakoki dayawa wanda sun hada da African Gold vol 1 zuwa 7, Akwai Iconic sounds of Africa itama tazo a vol daban daban.

Wakokin Ala da suka shahara sun hada da:

Wakokin Ala da suka shahara sun hada da: 
Wakokin Ala da suka shahara sun hada da:
  •  Buri Uku a Duniya
  • Hangen Dala
  • Bakan dabo
  • Wanzami
  • Shahara
  • Lu’u Lu’u
  • Isah bello ja
  • Ina Jama’ar Kano
  • Ummi Momina
  • Na koma gida
  • Burutai
  • Ubangidana
  • Jami’a
  • Naci kasuwa
  • Bara a kufai
  • Bawan burmi
  • Sakarkari

Karramawar Aminu Alan Waka

Karramawar Aminu Alan Waka 
Karramawar Aminu Alan Waka

Alan waka yasamu karramawa daga wajaje daban daban wanda sun kunsa:

Karramawar digirin digirgir daga jami’ar CEGT na kasar Benin

Karramawar Jami’ar Ahmadu Bello Zaria

Karramawar masarautar Dutse da sarautar sarkin mawakan Masarautar Dutse

Sarautar dan Amanar Bichi

Da sauransu.

Hotunan Aminu Alan Waka

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Watch African Stories

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button