Biography

Cikakken Tarihin Rabiu Musa Kwankwaso, Rayuwarsa, Karatunsa, Aikinsa, Siyasarsa, Iyalensa, Gudumawarsa, Arzikinsa, Hotunansa

Cikakken Tarihin Rabiu Musa Kwankwaso

Labaranyau.com ta kawo cikakken tarihin Engr Rabiu Musa kwankwaso fara daga farkon rayuwansa, karatun sa siyasar sa da sauransu.

Cikakken Tarihin Rabiu Musa Kwankwaso
Cikakken Tarihin Rabiu Musa Kwankwaso

Rayuwar Rabiu Musa Kwankwaso

Rayuwar Rabiu Musa Kwankwaso
Rayuwar Rabiu Musa Kwankwaso

Kwankwaso shahararren dan siyasa ne Wanda riqe mukamai daban daban na siyasa. An haifeshi ranar 21 ga watan Oktoba na shekarar 1956 a garin Kwankwaso, Madobi. Mahaifinshi shine sarkin fulani kuma dagacin Kwankwaso. Mahaifinshi yayi riqe sarautar majidadin kano da sarkin madobi kamin rasuwar sa.

Karatun Rabiu Musa Kwankwaso

Karatun Rabiu Musa Kwankwaso 
Karatun Rabiu Musa Kwankwaso

Injiniya Kwankwaso yayi mafi yawan karatun sa ne a Jihar kano, fara da karatun firamare wanda yayi a firamaren Kwankwaso ya karasa a firamaren kwana na Gwarzo wudil craft school. Sai ya wuce gaba dan karatun sakandare a kano technical college.

Rabiu Kwankwaso ya wuce gaba dan karatun jami’a a kaduna polytechnic inda yayi national diploma da higher national diploma. Lokacin da yake Makaranta ya kasance shugaban dalibai, bayan zaben sa da sukayi ya jagoranci kungiyar dalibai na jihar kano. Ya kuma yi digirinsa na biyu a Middlesex Polytechnic na turai da kuma masters dinsa a fannin kimiyar ruwa a jami’ar Loughborough University of Technology inda ya kammala a shekarar 1985. Yayi digirin digirgir a jami’ar sharda a kasar india a shekarar 2022 ya yi Ph.D. in water engineering.

Aikin Kwankwaso

Aikin Kwankwaso 
Aikin Kwankwaso

A shekarar 1975, Kwankwaso yayi aiki da gwamnatin jihar kano inda yayi aiki da State Water Resources and Engineering Construction Agency. Bayan yayi aiki na shekara 17 kamin yayi ritaya sai da ya kai muqamin principal water engineer.

Siyasar Kwankwaso

Siyasar Kwankwaso 
Siyasar Kwankwaso

Rabiu Kwankwaso ya shiga harkan siyasa a shekarar 1992 a jam’iyar SDP, a wannan shekarar aka zabeshi ya zamo dan Majalisan tarayya na mazabar madobi jihar kano. Ya samu shahara a kasar bayan zaman sa mataimakin shugaban Majalisan tarayya tare da Yaradua. Kwankwaso ya samu zama delegate daga kano wajen kirkirar dokar kasa na 1995. Ya kuma koma jam’iyar DPN a lokacin mulkin Abacha.

A lokacin jagoran jam’iyar Malam Musa Gwadabe, tare da Sanata Hamisu Musa, Alhaji Abdullahi Sumaila da Kwankwaso suka koma PDP inda Kwankwaso yayi takara a 1999, sukayi zaben firamare da Alhaji kabiru Rabiu, Mukhtari Zimit, Abdullahi Ganduje kuma Kwankwaso ya lashe zaben. Kuma yayi gwamna a kano zuwa 2003.

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya zabeshi a matsayin ministan tsaro inda ya karba a hannun Theophilus Danjuma, zuwa shekarar 2007 ya ajiye aikin ministan dan takarar gwamna Amma baici zabe ba inda Alhaji Ahmed Garba Bichi ya maida gurbin sa a matsayin.

Obasanjo ya kuma zabe shi a wakilci najeriya a somalia bayan ya fadi zabe a 2007. Tsohon Shugaban kasa Yaradua kuma ya bashi mambar board na Neja delta development commission ya riqe muqamin kamin ya ajiye a shekarar 2010.

Daga shekarar 2011 zuwa 2015 yayi gwamna a jihar kano kuma yayi sanatan jihar kano ta tsakiya zuwa 2019. Kwankwaso ya koma jam’iyar PDP a shekarar 2018 inda yayi takarar shugaban kasa akayi firamare dashi yazo na hudu da kuri’u 158 bayan Atiku Abubakar mai kuri’u 1532, Amina tambuwal 693, Bukola Saraki 317.

Kwankwaso yayi mubayi’a wa Atiku da kuma alkwarin rashin takara, inda ya bar fili wa shekarau na yin sanata kuma ya goyin bayan Abba Yusuf kabir yayi Gwamna kuma ganduje ya lashe zaben a 2019. A shekarar 2022 Kwankwaso ya zama dan takarar shugaban kasa a Jam’iyar NNPP inda ya kuma zo na hudu bayan Tinubu da yaci zabe, sai Atiku sai Peter Obi a zaben da ta gabata na shekarar 2023.

Iyalen Kwankwaso

Iyalen Kwankwaso 
Iyalen Kwankwaso

Rabiu Kwankwaso Yana da aure kuma da yara, ya saki matar sa ta farko a shekarar 1999 inda ya auro ta biyu. Yara takwas din  daga matansa ne guda biyu, da wanda ya saka da wanda ke gidan.

Gudumawar Kwankwaso

Gudumawar Kwankwaso 
Gudumawar Kwankwaso

Engr Rabiu Musa Kwankwaso ya kirkiro da gidauniyar Cigaba mai suna Kwankwaso development Foundation, bayan ya bar kujerar sa na gwamnati a matsayin sa na gwamna dan taimaka wa yan jihar kano da najeriya baki daya.

Ta wannan gidauniyar, Kwankwaso Yana bada tallafin kudi wa yara dan yin karatu da kuma samo ilimi, bayan sun gama digirin su, dalibai 370 wanda suka samu tallafin sunyi karatu kuma sun dawo kasar a shekarar 2021. Dayawa daga cikin su bayan sun dawo sun samu aiki a kasa najeriya da kuma kasashen waje, ciki harda wanda suka samu aiki a kampanin BUA da Dangote.

Arzikin Kwankwaso

Arzikin Kwankwaso 
Arzikin Kwankwaso

Rabiu Kwankwaso Yana daga cikin masu kudi yan siyasa a najeriya, Yana da arziki kimanin Miliyan goma na dalar America.

Shafin Sadarwan Kwankwaso

Shafin Sadarwan Kwankwaso 
Shafin Sadarwan Kwankwaso

Rabiu Musa Kwankwaso Yana da shafin sadarwa a Twitter da instagram, inda yake da mabiya sama da 200,000. Domin bibiyar Rabiu Kwankwaso zaku iya bin shi a Twitter: @KwankwasoRM
Instagram: kwankwasorm.

Hotunan Rabiu Musa Kwankwaso

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Watch African Stories

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button