
Fitattun Jaruman Kannywood Masu Tashe a 2025
Masana’antar Kannywood na cigaba da bunkasa a kowace shekara, inda jarumai ke tasowa tare da nuna bajintarsu a fagen harkan fim.
A shekarar 2025, wasu jaruman sun fi haskakawa da farin jini a tsakanin masoya da masu kallo.
Ga jerin fitattun jaruman Kannywood masu tashe a 2025:
1. Ali Nuhu

Ali Nuhu, wato “Sarki Ali,” ya ci gaba da kasancewa a matsayinsa na babban jarumi a cikin manyan jaruman Kannywood.
A wannan shekarar 2025, yayi a fina-finai da dama kuma yana ba da horo wa sauran matasa masu tasowa a masana’antar Kannywood.
Haka kuma, ya ci gaba da jagorantar fina-finai masu Kyau, Ilmantarwa, da kuma kayatarwa.
2. Adam A. Zango

Adam A. Zango shima ya cigaba da haskakawa a masana’antar Kannywood, ya shirya fina-finai masu kayatarwa da fidda sababbin wakoki.
Har yanzu Adam A. Zango shahararren jarumi ne a Kannywood, kuma yana ci gaba da sumun masoya a shafukan sada zumunta.
Koda Kana bukatar: Jerin Jarumai 14 Mafiya Arziki A Kannywood 2025
3. Rahama Sadau

Rahama Sadau itace ta daya a cikin fitattun jarumai mata na wannan shekarar. Ta fito a fina-finai da yawa a Kannywood da Nollywood, wanda ya kara mata bajinta da farin jini.
kuma, ta bunkasa kasuwancinta na kayan kwalliya da tallace-tallace.
4. Hadiza Gabon

Hadiza Gabon tana cikin jaruman Kannywood mafiya tashe a 2025. Ta fito a fina-finai da yawa.
Tana taka rawan gani wajen taimakon al’umma ta hanyar gidauniyarta.
A wannan shekarar, ta samu karin farin jini saboda hazakarta a fagen fim.
Koda Kana bukatar: Sabbin Fina-Finan Kannywood Masu Tashe a Shekarar 2025
5. Garzali Miko

Garzali miko Matashin jarumi kuma mawaki, ya shahara a cikin shekarar 2025. Wakokinsa sun samu karbuwa sosai, ya fito a fina-finan da suka ja hankalin mutane da waya.
Garzali miko shima daya daga cikin jaruman da sukaafi samu masoya a shafukan sada zumunta.
6. Maryam Yahaya

Maryam Yahaya ta sake dawowa da sabon salo a shekarar 2025, inda ta fito a fina-finai da suka ja hankalin mutane.
Maryam Yahaya tayi fama da jinya a baya, amman ta dawo da kwarin gwiwa kuma ta zama daya daga cikin manyan jaruman mata mafiya shahara a wannan shekarar.
Koda Kana bukatar: Rayuwa da Tarihin Jaruman Kannywood
7. Umar M. Shareef

Umar M. Shareef, wato babban mawaki, kuma yayi fice a bangaren fina-finai ma.
A 2025, ya fito a sababbin fina-finai masu kayatarwa kuma ya cigaba da zama daya daga cikin fitattun manyan jaruman Kannywood.
8. Sani Danja

Sani Danja ya dawo cikin masana’antar Kannywood da sabon salo, inda ya fito a fina-finai da dama masu kayatarwa.
Sani Danja na daya daga cikin jaruman da suka dade a masana’antar amma har yanzu suna cigaba da jan hankalin masu kallo.
Kammalawa
Jaruman Kannywood sun ci gaba da nuna bajintarsu a fagen shirya fina-finai a shekarar 2025.
Wasu daga cikinsu sun shahara a Kannywood kadai, wasu kuma da Nollywood da sauran kasashen duniya.
Wannan yana nuna yadda masana’antar Kannywood ke bunkasa tare da ba da dama ga sababbin jarumai masu hazaka da juriya.