
Kyawawan Matan Kannywood 10 da sukafi tashe a wannan shekarar 2025 suna ƙayatar da masoya fina-finan Hausa da kyawunsu, basirarsu, da rawar da suke takawa a masana’antar Kannywood.
A duk shekara, wasu jaruman mata suna fitowa fili don ɗaukar hankalin jama’a da salon su na musamman da kuma rawar da suke takawa a cikin fina-finai masu kayatarwa.
A shekarar 2025, wasu daga cikin jaruman Kannywood sun yi fice sosai, sun jan hankali a masana’antar da social media kamar su Facebook, Instagram, TikTok da sauransu.
Wannan post zai kawo manyan jarumai mata guda goma da suka fi tashe a bana, waɗanda ke da kwarjini, kwarewa, da kuma tasiri a duniyar fina-finai.
Kyawawan Matan Kannywood 10 da Sukafi Tashe a Wannan Shekaran 2025
1. Firdausee Yahaya – Kyakkyawar Tauraruwa Mai Tasowa

Firdausee Yahaya ta kasance jaruma mai tasowa da ke jan hankalin masoya masu kallo saboda kyawunta da kwarewarta a fagen wasan kwaikwayo.
A shekarar 2025, ta samu matsayi na musamman saboda rawar da take takawa a wasu manyan fina-finai da kuma salon acting dinta mai kayatarwa.
2. Fateema Usman Kinal – Jaruma Mai Hazaka

Fateema Usman Kinal kyakkyawar jaruma a Kannywood da take tashe a bana. Bajintar da take takawa a fina-finan zamani da kuma rawar da take takawa a masana’antar sun sa ta zama ɗaya daga cikin taurarin da suka fi farin jini a bana.
Kana Bukatar: Shahararrun Tsofaffin Finafinan Kannywood 15 Masu Ban Mamaki
3. Maryam Booth – Fitacciyar Jaruma Mai Dimbin Kwarewa

Maryam Booth fitacciyar jaruma mai kyau, ta ci gaba da haskawa a masana’antar fina-finan Kannywood, inda take taka rawar gani a manyan fina-finai masu kayatarwa. A matsayinta na gogaggiyar jaruma, tana amfani da fasaharta wajen jawo hankalin masoya masu kallo.
4. Zarah Aliyu – Kyakkyawar Jarumar da Ke Jan Hankali

Zarah Aliyu kyakkyawar jarumar da ke jan hankalin masoya, ta kasance daya daga cikin jaruman da suka samu karbuwa sosai a 2025.
Kyawunta, ladabinta, da kwarewarta a fagen wasan kwaikwayo sun sanya ta cikin taurarin da ake matukar so a masana’antar Kannywood.
Kana Bukatar: Manyan Tashoshin YouTube na Kannywood: Tushen Nishaɗi, Labarai Masu Zafi, da Sabbin Fina-Finai Masu Kayatarwa
5. Zarah Diamond – Tauraruwa Mai Kyau da Basira

Zarah Diamond tauraruwa mai kyau da basira, ta samu matsayi mai girma a masana’antar Kannywood a wannan shekarar, tana taka rawar gani a fina-finai masu jan hankali.
Kyawunta da hazakar da take nunawa sun sa ta zama ɗaya daga cikin jaruman da suka fi tashe.
6. Rahama Sadau – Kyakkyawar Fitacciyar Jaruma

Rahama Sadau Kyakkyawar fitacciyar jaruma ba ta gushe wa a jerin manyan jaruman Kannywood da suka shahara a duniya.
Tana da ƙwarewa a bangarori da dama, kuma tana taka rawar gani a cikin manyan fina-finan Kannywood da Nollywood.
Kana Bukatar: Yadda Zaka Shiga Kannywood Ka Dawo Jarumi Ba Tare da Wahala Ba: Hanya Mafi Sauki
7. Nafisa Abdullahi – Kyakkyawar Tauraruwa a Masana’antar Kannywood

Nafisa Abdullahi ta kasance mai kayu kuma fitacciyar jaruma a masana’antar fina-finan Kannwood, tana daukar nauyin manyan fina-finai masu kayatarwa. Kyawunta da hazakarta sun ba ta matsayi na musamman a Kannywood.
8. Rukky Alim – Jaruma Mai Kyau da Kima

Rukky Alim Jaruma Mai Kyau da Kima, ta zama ɗaya daga cikin taurarin da suka fi tashe a bana. Tana taka rawar gani a fina-finai da yawa masu kayatarwa, inda take bai wa masoya masu kallo nishaɗi da farinciki.
Kana Bukatar: Jerin Sabbin Finafinan Kannywood Masu Kayatarwa Na Soyayya, Ban Dariya, Ban Tausayi Dana Tarihi 2025
9. Meerah Shuaibu – Jarumar da Ke Samun Karbuwa

Meerah Shuaibu tana da kayu sosai daga cikin jaruman da suka shahara a shekarar 2025, tana taka rawar gani a manyan fina-finai masu kayatarwa. Kyawunta da kwarewarta sun sanya ta cikin manyan taurarin Kannywood.
10. Maryam Yahaya – Kyakkyawar Jarumar da Ke Ci Gaba da Haskawa

Maryam Yahaya ta kasance Kyakkyawa daga cikin fitattun jaruman Kannywood. Tana taka rawa gani a manyan fina-finai da dama masu kayatarwa, kuma ta shahara a kafafen sada zumunta saboda kwarewarta da kyawunta.
Kana Bukatar: Dalilan da Yasa Jaruman Kannywood ke Komawa Nollywood
Kammalawa
Wadannan kyawawan ‘yan matan Kannywood 10 da Sukafi tashe a wannan shekaran 2025 sun samu farin jini ne ba kawai saboda kyawun halittarsu ba, har ma da bajintarsu a fagen wasan kwaikwayo.
Idan kuna son ci gaba da samun labarai masu kayatarwa kan shahararrun jaruman Kannywood da fina-finai masu tashe, ku ci gaba da bibiyar shafukanmu don samun sabbin bayanai masu ƙayatarwa!