
Kaftin Bruno Fernandes ya mayar da martani kan kalaman da mai kungiyar Manchester United, Sir Jim Ratcliffe ya yi.
Jim Ratcliffe ya soki wasu daga cikin ‘yan wasan kungiyar a bainar jama’a, yana mai cewa “ana biyan su fiye da kima” kuma “ba su da kyau.”
Ya ambaci manyan ‘yan wasa, musamman Casemiro, Rasmus Hojlund, Andre Onana, Jadon Sancho, da Antony, yana mai nuna rashin jin dadinsa a cikin wasanninsu har ya zuwa yanzu.
Kalaman Ratcliffe sun haifar da cece kuce da yawa game da samun kimar ‘yan wasan bisa kan kudin da aka kashe kan wadannan sa hannun.

Martanin Kaftin Bruno Bisa Sukar Jim Ratcliffe Akan ‘Yan Wasa Maras Amfani!
Kaftin Fernandes ya bayyana rashin jin dadin sa sosai ga wadannan kalamai.
Bayan ya jagoranci kungiyar Manchester United zuwa wasan daf da na kusa dakarshe a gasar cin kofin zakarun Turai ta Europa da ci uku 3.
Dan wasan tsakiya na Portugal ya ce;
“Ba abu ne mai kyau, jin wasu sukar ba, a fili. Ba na jin wani dan wasa yana son jin suka ko kuma a gaya masa cewa be isa ba, ko an biya shi fiye da kima, ko wani abu.”
Duk da haka, Kaftin Fernandes ya fahimci cewa ya rage ga ‘yan wasan su mayar da martani a filin wasa da kuma horo, yana mai cewa;
“Muna buÆ™atar nuna kanmu kowace rana a horo, kowace rana da muke da wasa. Ba za mu iya hutawa a wannan kulob din ba.”
Ya kuma amince da manyan matakan da ke tattare da buga wasa a Manchester United, ya kara da cewa;
“Kun san akwai babban matsayi, babban lura da kuke samu daga kafafen yada labarai, daga ko’ina. Kuna bukatar ku gane cewa ako wani lokaci kuna bukatar sanya hankalinku kan wasanku, kuna kuma kokarin inganta kanku.”
Duk da sukar da aka yi, Kaftin Bruno ya tunatar da kowa cewa kwangila yarjejeniya ce tsakanin ‘yan wasan da kulob din.
“Kowa yana da nasa kwantiragi, kungiyar ta amince da yin kwantiragin a lokacin da suka zo nan, ko kuma lokacin da suka yi sabon kwantiragi, komai ya shafi kanku ne, wanda ke tabbatar da cewa zaku iya zama muhimmi a kungiyar.”
A Takaice
Martanin Kaftin Bruno Fernandes ya nuna sadaukar da kai don tabbatar da kimarsu, duk da matsin lamba da kuma matukar muhimmanci ga ‘yan wasan Manchester United.
Sun san tsammanin su na da yawa, amma a shirye suke su tashi don fuskantar kalubale kuma su nuna dalilin da ya sa suka cancanci saka sanannen jar rigar.
Highlights na Manchester United vs Real Sociedad – Europa League
Labarai Masu Alaqa:
- Ingancin Bruno Fernandes A Matsayin Kaftin na Man United Har Zuwa 2030!
- Matakin Bruno Fernandes Na Karya Tarihi a Manchester United (2025)
- Masu Daukan Mafi Ƙarancin Albashi A United (2025)
- ‘Yan Wasan Dasuka Fi Kowa Kwasan Albashi Me Tsoka a Manchester United (2025) – Abin Mamaki
- Ƙananan Yaran Da Man United Zata Ƙarasa Kakan 2024/2025 (Season) Dasu Dan Dole!